Connect with us

TATTAUNAWA

Garkame Gidajen Mai Ya Bude Sabon Babin Haraji A Kano –Shugaban IPMAN

Published

on


Garkame gidajen wasu mai a Kano da jami’an haraji su ka yi karkashin jagorancin mai ba gwamnan Kano shawara a kan harkar tattara kudaden shiga na gwamnatin Kano, Hon. Habibu Sale Mailemo, ya bude wani sabon shafi tsakanin masu harkar haraji da kuma masu gidajan mai a Kano.
Shugaban kungiyar masu gidajan mai da sayar da albarkatun man fetur masu zaman kansu, wato independence Petroleum Marketing Association Of Nigeria IPMAN a takaice Alhaji Bashir Dan Malam ya bayyyana cewa harkar man Fetur harkace mai mahimmanci a tsakanin al’umma wacce take dauke da dubban daru ruwan al’umma musamman matasa a wannan Jaha da kasa baki daya dan haka ya kamata Gwamnati ta dau abinda mahimmanci kuma a daina sa Yan Siyasa a cikin wannan lamari na karbar Haraji domin harkar mai a yau gawa ma tana amfanuwa da harkar man Fetur dan haka ba abune da za ayi sako sako ko kama karya a cikin wannan harka ta Man Fetur ba.
Alhaji Bashir Dan Malam wanda shi ne shugaban IPMAN na shiyyar Arewa maso Yamma da ta kunshi wadannan Jahohi irin su Kano, Katsina, Kaduna, Jigawa, Bauchi, Yobe, Yola ya bayyana cewa harkar haraji Mai kamata a rikasa Yan juwa juwa a cikin harkar haraji wanda kullum tunaninsu abin da zasu samu susa a aljihunsu shi ne suke tunani kullum. Dan Malam ya kara da cewa su abinda suka sani a matsayinsu Yan Kasuwa shi ne biyan Haraji shi ne Sarki haka abin yake a Dokar Kasa haka yake a kasashen Turai amma baisan Dokokin Haraji na Kano ba dan haka suna bukatar abasu kwafi na Dokokin Haraji na Kano domin ilmantar da membobinsu na IPMAN.
Dan Malam ya kara da cewa su dai masu bin doka da Oda ne kuma masu biyayya da Gwamnati ne duk da bai san adadin Gidajan Man da Hukumomi suka garkame ba yanzu a Kano ya umarci duk gidan man da aka garkame ka da su budeshi su saurari Kungiyar akan matakin da ta dauka na tattaunawa da masu ruwa da tsaki akan wannan lamari.
Haka kuma ya koka akan yadda aka nuna san zuciya ta hanyar karyar da farashi da akayi wa diyya na wasu Gidajan Mai akan kudi da bai taka kara ya karya ba duk da da anyi Magana diyya mai daraja kuma amfado da ita a kankanin lokaci kuma a Gwamnati guda. Haka kuma ya bayyana cewa su dai IPMAN akan doka da oda suke kuma a sani cewa basu da ikon kara ko kwabo akan farashin Man Fetur yadda doka tace su siyar haka suke siyarwa tunda a kwai hukumomi masu lura da abubuwan da ke tafiya a wannan Sana’a ta Man Fetur.
A karshe ya yabawa Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje akan kafa kwamitin Gaggawa domin kamo bakin zaran akan cacar baki da ta barke tsakanin Hukumomin Haraji karkashin Jagorancin Hon. Habibu Sale Mai Lemo da kuma kungiyar IPMAN karkashin jagorancin Alhaji Bashir Dan Malam Kano sai dai kuma wakilin Leadership A Yau Lahadi yayi kokarin jin ta bakin mai ba Gwamna Shawara kan harkar Haraji a Kano Hon. Habibu Sale Mai Lemo Fagge abin ya ci tura.


Advertisement
Click to comment

labarai