Connect with us

LABARAI

2019: Jamilu Gwamna Ne Zai Iya Zama Magajin Dankwambo –Sarkin Yarbawan Gombe

Published

on


A lokacin da zabubbukan shekarar 2019 ke ta kara karatowa Sarkin Yarbawan jihar Gombe Alhaji Abdulrahim Jima Alao Yusuf, ya bayyana dan takarar gwamnan jam’iyyar PDP a jihar Gombe Alhaji Dakta Jamilu Isiyaku gwamna da cewa shi ne yafi cancanta da zama magajin Dankwambo.
Alhaji Abdulrahim Jima Alao Yusuf, ya bayyana hakan ne a Gombe a lokacin da yake zantawa da Leadership A Yau Lahadi, inda yace mai tunani da hangen nesa kuma wanda yake gina al’umma kamar Jamilu Isiyaku Gwamna ne ya kamata a zaba ya zama gwamnan Gombe idan Allah ya kai mu 2019.
Sarkin Yarbawan Gombe, ya kuma ce a guji zaben tumun dare dan kawai wasu mutane da suka fito dan su nuna suna da kudi da zarar an zaben su fa an dai na ganin su kenan balle ma su sauraron jama’a kan matsalolin da suka dace hakan yasa yake kiran al’ummar jihar Gombe da suyi zurfin tunani da hangen nesa.
Ya ce mai tsari wanda aka san cewa yana taimakon jama’a wajen gina jiha da al’ummar ta tun farko ne ya dace ba wanda zai zo rana a tsaka ya yiwa mutane zagin baki ba.
A cewar Alhaji Abdulrahim Jima Alao Yusuf, Alhaji Dakta Jamilu Isiyaku Gwamna mutum ne da yake da ilimi ya kuma yi gwagwarmaya sosai ya san matsalolin jihar kuma shi ne kowa yasani ya taimaki jama’a tun yana hukumar samar da ruwan sha na Water board har yanzu ya zama babban Darakta a kamfanin hukumar samar da hasken wutar lantarki ta KEDCO.
Ya kuma ce yana da kyau duk wanda za’a zaba a shaida masa cewa yana da kyau ya samarwa da kananan hukumomi yancin su domin rage yawan sintirin mutanen kauyuka zuwa cikin gari domin idan kananan hukumomi suka sami yanci suna aiki za su ragewa gwamnati dawainiya mai yawa.
Sarkin Yarbawan Gombe, ya kaara da cewa idan dai kishin Gombe ake magana to a cire son zuciya da kyashi a zabi Sardaunan Gombe Alhaji Dakta Jamilu Isiyaku Gwamna shi ne zai cirewa jama’ar Gombe citse a wuta.
Har ila yau ya kara da cewa duk wanda ya kwana a Gombe ya tashi yasan Jamilu bai da banbancin siyasa ko na addini bare na kabilanci kowa nasa ne kuma dama a siyasa irinsu ake so ba wanda zai zo ya raba kan jama’a ba.
A duk yan takarar da suke Gombe a duk jam’iyyun siyasar da ake da su babu kamar Jamilu Isiyaku Gwamna saboda yasan ya kamata kuma shi ne dan takarar da yake da hangen nesa da zai iya zama gwamna a 2019 idan jama’a suka yarda suka zabe shi.
Alhaji Abdulrahim Jima Alao Yusuf, ya yi amfani da wannan damar ya yi kira ga mata da matasa da kowa ma na cewa duk wanda bai da katin zabe ya hanzarta yaje ya yanka domin shi ne yancin sa dan idan mutum bai da katin zabe ba yadda za’ayi ya zabi wanda yake so.
Ya kuma jawo hankalin jama’a da cewa su dai na sayar da yancin su na zabe akan naira dubu biyar ko kasa da haka a lokacin zabe su daure su zabi cancanta dan sayar da kuri’a lokacin zabe ba yadda za’ayi ka kalubalenci shugaban ka dan baka zabe shi ba, sannan kuma yace a guji yin sak saboda yin sak ya kan debo tarkace da yawa a tsaya a zabi mutum nagari.
Sarkin na Yarbawa yace ba a iya gwamna ba tun daga kan kansila zuwa shugaban kasa cancanta za a zaba dan wasu da yawa sukan zo suna nunawa mutane cewa sun iya suna zagin baki amma idan aka zabe su ba za’a sake ganin su ba sai lokacin wani zaben.
Daga nan sai yace su dai mutanen Gombe fatar su shi ne Dakta Jamilu Isiyaku Gwamna ya amince ya fito takara dan shi ne wanda yafi cancanta da zama Gwamnan Gombe wanda kuma rashin fitowar sa zai iya zame musu asara.


Advertisement
Click to comment

labarai