Connect with us

LABARAI

Za A Fara Allurar Riga-kafin Foliyo  A Kaduna

Published

on


Kungiyar yan jarida mai yaki da cutar foliyo reshen jihar kaduna JAP ta sanar da cewar yau Asabar 30 ga watan Yuni za a fara yin allurar riga-kafin foliyo, har zuwa ranar 3 ga watan Yulin 2018.

Shugaban kungiyar Alhaji Lawal Dogara ne ya bayar da sanarwar,inda ya ce, za a gudanar da shirin a gida-gida da kasuwanni da tashoshin motoci da manyan hanyoyi da sauran su haka gwamnatin jahar  ta hanyar hujumar matakin lafiya ta farko, ta shirya tsaf don cin nasarar shirin.

Ta shawarci iyayen yara da kuma masu kula da yara da su tabbatar da sun miika ‘ya’yansu don yi masu riga-kafin.

Kungiyar ta yi kira ga malaman addini da sarakunan gargajiya kada su gajiya a kan goyon bayan da suke bayarwa don samun cin nasarar yaki da cutar a daukacin fadin jihar,inda ta kara da cewar an kammala dukkan shirye-shiryen da suka dace don cim ma nasarar aikin.

 


Advertisement
Click to comment

labarai