Connect with us

TATTAUNAWA

Agara Na Neman Gwamna Wajen Allah Ne A Nasarawa In ji  Yusuf Musa

Published

on


Yusuf Musa Umagi shi ne Jagoran yakin neman zaben Honarabul Silas Ali Agara a matsayin Gwamnan jihar Nasarawa, a babban zabe mai zuwa na shekarar 2019. A  hirar da ya yi da wakilinmu Zubairu T M Lawal a ofishinsa da ke garin Lafiya ya bayyana dalilan da suka sanya al’umma ke bukatar Mataimakin Gwamnan ya gaji kujerar Gwamnan a zabe mai zuwa da kuma irin ci gaban da jihar Nasarawa za ta amfana ta hannunsa.

Da farko masu karata za su so su ji sunanka da matsayinka

Sunana Yusuf Musa Umagi ni ne jagoran yakin neman zaben Honarabul Silas Ali Agara mai neman Gwamnan jihar Nasarawa.

 

Ko za ka bayyanawa masu karatu dalilin da ya sa kuka ni me Honarabul Silas Agara ya tsaya takarar Gwamnan jihar Nasarawa?

A gaskiya sanin kowane duk lokacin da al’umma suka samu shugaban nagari to komai zai zo da sauki ba za su samu hayaniya ba. Shi wannan dantalikin dalilin da ya sa muka bukaci da ya yi mana takarar Gwamnan saboda kwarewansa da cancantarsa tun lokacin da aka fara mulkin tarar hula a kasaran ake damawa da shi cikin Gwamnatin Jihar Nasarawa.

Lokacin Gwamnatin Abdullahi Adamu ya rike mukami kuma lokacin Gwamnatin marigayi Ali Akwe Doma ya rike mukami. Sanan tun farkon Gwamnatin Umar Tanko Al-makura yana rike da mukami a shekarar hudun farko ya kasance mai ba da shawara na masamman daga bisani aka tsayar da shi dan takarar Mataimakin Gwamnan jihar Nasarawa yanzu da shi ake damawa ya san ciki da waje da damuwar jihar Nasarawa.

Shi ya sa muka bukaci da ya tsaya mana takara saboda shi ya san inda aka yi da inda za aka rasa dama inda ba a yi ba. Yana da gogewa ya yi aiki da Gwamnoni uku kuma an gama lafiya da shi ka ga shi ya cancanta musa a gaba.

 

Wasu na ganin yana da karancin shekaru?

Abin ba na shekaru ba ne gogewa da sanin aiki ake ni ma ba yawan shekaru ba . kuma ai dokar kasa bai hana shi niman Gwamna ba saboda shekaru muna son yanzu haka yana niman shekara hamsim amma kuruciyar aiki gare shi kuma idan kana bukatar aiki na kwarai ka kawo mai karancin shekaru.

Ina amfani shekaru babu hankali wani za ka same shi da yawan shekaru amma yana wasan kasa wani kuma za ka same shi da yawan shekaru amma yana kida da rawa wani za ka same shi da karancin shekaru amma yana aiki irin na dattawa halayyar mutanin kirki to wanan ake so ba tarin shekaru ba.

 

Wasu na fadin cewa akwai gogagun ‘yan siyasa a gabanku shin ko za ku kai labari?

Gogewa a siyasa ba yana nufin yawan shekaru ba ne. Su waye gogagun ‘yan siyasa da ke niman kujerar Gwamnan jihar Nasarawa akasarinsu ma’aikatan Gwamnatine da suka ajiye aiki wasu kuma harkan kasuwancinsu suke yi yaushe suka fara siyasa da za a ce gogaggu. Gogagge shi ne wanda aka dade ana damawa da shi cikin harkan siyasa kuma duk cikansu waye ya kai Mataimakin Gwamnan Silas dadewa cikin harkar siyasa? Kuma wa ya kai shi gogewa da sanin aikin Gwamnati a tsarin siyasa?.

 

Yanzu harkar siyasa ta masu kudi ne ana ganin akwai miloniyoyi da suka fado cikin harkar siyasa a Nasarawa da za su iya taka maku birki ya ya kake gani?

Haka ne siyasa da kudi ake yinta amma wani lokacin kudi ba ya kai mutum ga nasara sai dai halaye da kyawawan dabi’u da alheri da mutum ke sukawa ga al’umma. Akwai ‘yan siyasa da yawa da suke da kudi kuma suna kan mulki amma kudin nasu bai iya ba su damar cin zabe ba sun fadi. Akwai kuma wadanda ba su da kudin amma suna da kyakkyawar alaka da al’umma da aka yi zaben sun yi nasara. Duk da ana cewa mu talakawa ne ba mu da kudi muna da daidai gwargwadon wanda za mu yi amfani da shi gurin al’umma.

 

Wasu na cewa kuna bukatan Gwamna Al-makura ne ya tsaida Silas Agara a matsayin Gwamna?

Wannan ba gaskiya ba ne mu dai mun san Silas Ali Agara yana neman kujerar Gwamna ne gurin Allah Muna san Gwamna Umar Tanko Al-makura mai gidanmu ne kuma mun tabbata shi mutumin kirki ne ba ya wariya kuma ba ya kama karya ba zai danne wannan a kasa ya dauko wani ya dora a kansa ba. Kuma muna son Tanko Al-makura ya san muna neman Gwamna duk da cewa, akwai wadanda suke kokarin ganin cewa ya hana mu, shi ya sa suke ta cece-kuce cewa muna neman ya ba mu, “mu wurin Allah muke nema, idan Allah ya ba mu shi ne fatanmu kuma Tanko Al-makura ubangidanmu ne muna tare da shi dari bisa dari muna masa biyayya”.

 

Wadanne tanajikuke da shi idan kun samu gwamna da za ku yi wa al’ummar jihar Nasarawa?

Alhamdu Lillahi, yau a jihar Nasarawa kowa ya san Gwamna Al-makura ya yi aiki, amma duk dan’adam tara yake bai cika goma ba, duk ayyukan da mutum zai yi koda zai shekara ashirin ne a kan mulki akwai wajen da duk inda aka kai da aiki sai ka ga wani wurin aiki bai ishe su ba. Wasu wuraren ma ba a yi ba wasu wuraren kuma ba a kamala ba.

Amma Agara duk ya san da wannan saboda ana yi tare da shi ne. Ya san wuraren da aka kammala aiki ya san inda ba a kammala ba, ya san inda ake bukatar wani abu daban.

Kuma idan mun zo inda aka fara za mu kammala kuma inda ba a yi ba za mu yi. Kamar bangaren ilimi, kowa ya san rawar da Al-makura ya taka wajen gina fannin ilimi an gyara makarantu an gina benaye a kowace karamar hukumar an gina makarantu na zamani benaye kuma burinsa kowane yaro a jihar Nasarawa ya samu ilimi mai inganci ka ga idan Silas Agara ya zama Gwamna daga nan zai dora yaga yayi kokari an samar da ilumi mai inganci cikin wanan Jihar.

Aba yara ilumin zamani a sanya Kwamfutoci a manyan makarantu da kanana yara da manya su ci gajiyar gwamnati.

Sannan ka duba yadda Al-makura ya gyara gaba dayan jihar Nasarawa yau duk inda hedikwata jihar ya kai ko’ina a kasar nan hedikwatar jihar Nasarawa ta kai. A kudurin Tanko Al-makura bayan hedikwatar kananan hukuma ita ma a gyarata a sauya fasalinta. Kuma an fara idan Allah yasa Silas Ali Agara ya zama Gwamna karasawa za a yi.

Bangaren harkan noma kamar yadda Gwamna Al-makura ke kokari wajen bunkasa harkan noma a nan jihar haka mu ma za mu himmatu wajen ganin komai ya ci gaba kamar yadda aka fara . manoma da makiyaya za su amfana da kayan amfannin gona taki da sauransu su ma makiyaya a kula da damuwansu a kuma tsara yanayin zaman takewarsu ta yadda zaman lafiya zai kara inganta a tsakaninsu.

Harkan kiwon lafiya kamar yadda Gwamna Al-makura yake ci gaba da gina Asibitochi a jihar idan har ba a karasa aikin ginin ba idan Silas Agara yazu zai yi kokkrin karasawa ne wanda aka gama shi kuma a duba mene ne damuwarsu a samar musu.

Kamar yadda Al-makura ya inganta jin dadin ma’aikata a jihar Nasarawa muma haka za mu daura duk inda ma’aikaci yake zai yaba kamar yadda ake masa.

 

Daga karshe wane kira kake da shi ga sauran ‘yan takara masamman na jam’iyyar APC?

Sauran yan takara suyarda Allah ne ke ba da mulki, sanan su sani duk shugaba akwai hakin jama’a a kansa. Sanan ina rokon ‘yan takara da su kai hankali nesa ka da a yi siyasar ko a mutu ko a yi rai. sannan su yi hakuri idan Allah ya ba Silas su bi shi ka da sun duba kankantar shekarunsa.

 


Advertisement
Click to comment

labarai