Connect with us

LABARAI

Yau Majalisa Ke Tantance Sabon Mataimakin Gwamnan Bauchi

Published

on


A yau Juma’a ne majalisar dokokin Jihar Bauci za ta gudanar da zama na musamman domin tattance Abdu Sule Katagum, wanda Gwamnan Jihar Muhammad Abdullahi Abubakar, ya gabatar da sunansa a matsayin wanda yake son ya kasance masa mataimaki.

Hakan ya biyo bayan ajiye kujerar ce da tsohon mataimakin gwamnan jihar Injiniya Nuhu Gidado, ya yi a ranar 23 na watan Mayun 2018.

Wakilinmu ya labarto cewar, hakan ya biyo bayan wata zazzafar  muhawara ce da majalisar ta yi a ranar Laraba dangane da zaben mataimakin gwamnan da gwamnan Jihar ya yi, inda majalisar ta tike kan cewar shi wanda aka zaban wato Abdu Sule Katagum, ya hallara a gabanta a ranar Juma’a domin tantance shi.

Wakilinmu ya labarto kan cewar a idan majalisar ta amince masa bayan ta gama tantance shi ya zama sabon mataimakin gwamnan Jihar Bauci a karkashin gwamnatin APC, idan kuma majalisar ta ki amince masa zai yi tafiyarsa.

A yau Juma’ar dai majalisar za ta tantance Arc Abdu Katagum, walau ya zama mataimakin gwamnan Bauci ko akasin hakan.

Gabanin gwamnan ya fidda sunan Arc Abdu Katagum, a matsayin wanda zai maye gurbin Nuhu Gidado, Abdu Katagum shi ne shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin Jihar Bauci.


Advertisement
Click to comment

labarai