Connect with us

LABARAI

Obasanjo Ya Yi Kiran Samar Da Mafita Kan Kashe-Kashe A Nijeriya

Published

on


A sakamakon yawaitar kashe-kashen da ke ci gaba da aukuwa a Jos da ke cikin Jihar Filato, tsohon shugaban kasar Nijeriya Cif Olusegun Obasanjo, ya shaida cewar dole ne a daidaito da lamarin hade da sanya komai kan gabarsa domin kawo mafita mai dourewa kan matsalolin shekar da jinin al’umman kasa.

Kamar yadda tsohon shugaban kasar ke cewa, matsalolin mutane na bukatar mafita ne daga su mutanen, don haka ne ya shaida cewar dole ne a samar da mafita mai dorewa da zai kawo karshen kashe-kashe a wasu yankunan kasarnan.

Obasanjo, wanda ke jawabi a ranar Laraba a yayin da ya kai ziyarar ta’aziyya wa Gwamnan Simon Lalong a Jos.

Cif Obasanjo wanda ya kai ziyarar hade da iyalansa da kuma ‘yan tawagarsa, ya nemi gwamnatoci a dukkanin matakai su dauki matakan kawo karshen shekar da jinin bayin Allah a fadin kasarnan.

Ya ce, “Abin takaici ne gaya a ce irin wannan mummunar al’amari na ci gaba da faruwa a kasarnan.

“Ina da yakinin wannan matsalar ta shafi mutane ne, don haka su mutane din su ne za su nemo wa mutane mafita kan matsalolin.

“Don haka ya kamata ne a zauna a samar da mafita, mafita kuma mai dorewa wadda zai kai ga kawo karshen yawaitar kashe-kashen da ake yawan samu a fadin kasarnan.

“Ina fata, ina kuma rokon gwamnatin tarayya ta yi aikin hadaka da gwamnatocin Jihohi, kananan hukumomi da sauran al’umma domin fitar da mafita da kawo karshen ababen da suke janyo kashe-kashen rayuka babu gaira babu sabar,” A cewar Cif Obansajo.

Tsohon shugaban kasar, ya yi addu’ar Allah kawo mafita kan lamarin, hade da neman jama’a su ci gaba da baiwa zaman lafiya fifiko.

Da yake maida jawabinsa, Gwamnan Filato S. Lalong,  ya jinjina wa Obasanjo a bisa samun zarafin zuwa Jihar domin jajanta wa gwamnati da jama’an Jihar da lamarin ya shafa kai tsaye.

Simon Lalong ya nuna takaicinsa kan yadda ake yawaitar samun tashin-tashina a tsakanin al’ummar Fulani da Birom, inda ya nemi dukkanin bangarorin su yi kokarin sanya zaman lafiya a gabansu.

 


Advertisement
Click to comment

labarai