Connect with us

LABARAI

Mai Babur Ya Kashe Dan Jarida A Bauchi

Published

on


A shekaran Jiya Labara ne wani matukin mashin roba-roba ya kade wani dan jarida gami da hallakasa har lahira a Bauchi.

Dan jaridar da ya gamu da tsautsayin dai shine Malam Alhassan Yusuf wakilin jaridar ‘New Telegraph Newspaper’ a Bauchi.

‘Yar uwan mamacin dan jaridar, Jummai Yusuf ta shaida mana cewar dan uwan nata dan jaridar ya gamu da bugewar mashin din ne a titin Wunti da ke tsakiyar jihar ta Bauchi a sakamakon tsula gudun tsiya da direban mashin din ya ke yi a yayin da marigayin ke kokarin tsallake kan titin zuwa daya barin.

‘Yar uwan mamacin ta shaida cewar an yi kokarin hanzarta da dan uwan nata zuwa asibiti amma daga bisani rai yayi halinsa a lokacin da ake tare-taren ceto rayuwar tasa.

LEADERSHIP A Yau, Juma’a ta labarto cewar marigayi Alhassan Yusuf ya rasu yana da shekaru 45 a duniya, ya tafi ya bar mace daya da kuma ‘ya’ya shida a gidan nan na duniya.

An yi masa sutura hade da kaisa makwancinsa na dindindin ne a Jiya Alhamis, inda ‘yan jarida da dama suka halarci wannan jana’izan nasa.

Wakilinmu ya shaida mana cewar gabanin wannan hatsarin na mashin ta auku da marigayin, Alhassan yana da kosashen lafiya ba tare da wata cutar da take barazana wa rayuwarsa ba, ya koma ga mahaliccinsa ne a sakamakon wannan bugewar da mashin din ta yi masa.

Babban Kakakin gwamnan Jihar Bauchi, Malam Ali M. Ali ya nuna kaduwarsa gaya kan rashin dan jarida abokin aikin.

Ali M. Ali wanda ya nuna alheninsa a lokacin da ke tattaunawa da wakilinmu, inda ya bayyana sa a matsayin mutum mai hakuri, ya yi addu’ar Allah ya gafarta masa ya kuma jikansa.

Wasu abokan aikinmu da muka ji ra’ayinsu a kan marigayin sun nuna damuwarsu kan  rashin abokin aikinsu.

Najib Sani wanda shine wakilin jaridar Blueprint a Bauchi ya nuna alheninsa kan rashin abokin aikiin, “Na jijjiga gaya a lokacin da na samu labarin rasuwar Alhassan Yusuf, a ranar da babur din nan za ta bugeshi mun hadu da shi a Wunti muka gaisa. Kai duniyar nan ba abun komai bace, Allah ya jikansa.

“Mun jima muna aiki tare da shi, a kowani lokaci hakurinsa da juriyarsa ta fi bayyanuwa mana, muna jimamin rashin abokin aikinmu, Allah jikansa ya gafarta masa,” In ji Najib Sani.

Wakilinmu ya shaida mana cewar Alhassan Yusuf ya kuma taba aiki da jaridar Bauchi Lokaci Ya Yi, gabanin ta daina fitowa. Ya fara aiki da jaridar New Telegraph Newspaper tun da jimawa. Allah jikansa.

Wata majiya ta shaida mana cewar an rigaya an kame dan roba-roban da ya kadeshin, inda wasu majiyan suka shaida mana cewar yayi goyon mutane biyu a mashin din hade da gudu na kece raini.  

 


Advertisement
Click to comment

labarai