Connect with us

LABARAI

Kotu Ta Wanke Sule Lamido

Published

on


Babbar kotun da ke zamanta a Dutse, shalkwatar Jihar Jigawa, a jiya ne ta salami tare da wanke tsohon gwamnan Jihar Alhaji Sule Lamido, wanda ke fuskantar tuhuma a gabanta tun a shekarar 2017, kan karar da gwamnatin Jihar ta Jigawan ta kai shi.

Gwamnatin Jihar ta Jigawa ta kai tsohon gwamnan kara ne gaban kotun majistare ta II da ke Dutse, bisa zarginsa da haddasa tayar da tarzoma, da aikata laifi gami da bata suna.

Lauyan tsohon gwamnan, Barista Yakubu Ruba, tun da farko ya kalubalanci kotun ne kan rashin hurumin da take da shi na tantance gyare-gyaren da aka shigar a cikin karar, inda ya ce yin hakan ya saba wa sashe na 141 na dokokin Jihar Jigawa.

Alkalin da ke shari’ar, Usman Muhammad Lamin, sai ya kore maganan Lauyan tsohon gwamnan, inda ya ce, ba wani abu da aka yi wanda ya saba wa shari’ar, ya kuma yi umurni da a ci gaba da sauraron shari’ar. A kan hakan ne, Lauyan na Sule Lamido, ya sake neman wata bukatar a bisa wacce ya gabatar tun da farko, inda ya nemi kotun da ta dage sauraron shari’ar.

Da suke yanke hukunci, alkalan kotun, Ahmed Musa Gumel, Umar Sadik da Abdulhadi Sulaiman, sun salami tsohon gwamna Sule Lamido ne tare da wanke shi daga dukkanin wata tuhuma mai kama da hakan, kamar yadda Lauyan na shi ya nema tun da farko.


Advertisement
Click to comment

labarai