Connect with us

LABARAI

Gwamnatin Bauchi Ta Dakatar Da Mukaddashin Shugaban Karamar Hukumar Ningi

Published

on


Gwamnatin Jihar Bauci, ta dakatar da mataimakin shugaban riko na karamar hukumar Ningi, Alhaji Rabo Habu, a sakamakon rashin samun sahhalewa daga majalisar dokokin Jihar, don tantancewa gabanin amsar rantsuwar kama aiki.

Wannan zancen ya fito ne daga fadar gwamnatin Jihar Bauci, a cikin wata kwafin sanarwar manema labaru dauke da sanya hannun Sakataren gwamnatin Jihar Bauci, Muhammad Nadada Umar, wanda ya raba a ranar 26 ga Yulin 2018

Ya ce, umurnin dakatawar ta zo ne a sakamakon rantsuwar kama aiki da mataimakin kantomar ya yi ba tare da zuwa majalisar dokokin Jihar a tantance shi ba, don haka ne majalisar ta umurci Alhaji Rabo Habu, ya kaurace wa ofishinsa har sai majalisar ta sake tantance shi da kuma sake ba shi sabon takardar kama aiki.

Sanarwar tana cewa, “Watanni kadan da suka gabata, Alhaji Rabo Habu, ya amshi rantsuwar kama aiki a matsayin mataimakin shugaban karamar hukumar Ningi ba tare da amincewar majalisar dokokin Jihar Bauci ba.

“Don haka, sunan Alhaji Rabo Habu, mun sake tura shi zuwa majalisar dokokin Jihar Bauci domin tantancewa.

“Don haka Alhaji Rabo Habu, muna umurtarsa da ya zakuda daga ofis a matsayin mataimakin shugaban karamar hukumar, har sai an samu sahhalewa daga majalisar dokokin Jihar Bauci. Idan majalisar ta amince masa za a sake ba shi takardar kama aiki gadan-gadan,” A cewar sanarwar gwamnatin Jihar.

 


Advertisement
Click to comment

labarai