Connect with us

TATTAUNAWA

Burina In Biya Wa Al’ummar Bauchi Bukatunsu – Dakta  Aliyu Tilde

Published

on


Jumma’ar da ke da kirki tun daga Laraba ake gane ta wannan ita ce Karin Magana da yawancin jama’a masu magana da harshen hausa ke yin amfani da ita idan suka gani wani abin alkhairi ya dosu’su, saboda sun san an dade da sanin halin kirki  na shi abin da suka hango da idanunsu na manya.

Wannan karin magana ita ce yanzu ake ji a bakin yawancin mutane masu yin zabe a mazabar Bauchi ta kudu, tun lokacin da Dr. Aliyu Tilde ya bayyana aniyarsa  ta tsayawa takarar kujerar dan majalisar dattawa ta Bauchi ta kudu, don cike gurbin kujerar da dan majalisar dattawa na mazabar wanda marigayi Sanata Ali Wakili da Allah yayi wa rasuwa watannin da suka gabata ya bari, kuma a bisa kyakkyawar fata da suke yi idan har Allah yasa aka zabe shi zai yi shugabanci nagari na cika wannan gurbin a karkashin SDP.

Wannan yasa wakilimmu dake Jos LAWAL UMAR TILDE, ya yi tattaki zuwa gidansa a garin Tilde Fulani, don sanin shi  ko wanene shi da burinsa na tsayawa da manufofinsa idan Allah yasa ya lashe zaben ga dai yadda hirar tasu ta kasance.

Dokta kasancewar kana daga cikin na baya bayan nan da suka bayyana niyar tsayawa takarar wannan kujera ta Bauchi ta Kudu ko masu karatu zasu san ko wanene kai?

Suna’na Aliyu Usman Tilde an haife ni a garin Tilden Fulani a shekarar 1960, sunan babana Shehu Usman [mai-akwala] daga silar Ruga dan Dabo Titi. Wani bafilatani da ya zauna a kasar Toro cikin jihar Bauchi da lardin Lere a cikin kasar Zazzau tun kimanin shekaru 230 da suka gabata, kuma na fara da karatun Allo na Arabiya kafin na shiga Firamari ta Tilden Fulani a shekarar 1967-1973 daga nan na wuce Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya daga shekarar 1978 zuwa1982 inda nayi sa’a, na fito da Digiri na na farko a 1985-1988 nayi nasarar samun Digiri na biyu, kuma dukkan su biyun  nayi sune akan ilmin tsirrai ne. Sai kuma a shekarar 1989-1999 na sake yin Digiri akan fannin dabarun  aikin gona a Jami’ar Jos.

 

Ban sani ba ko Dokta ya taba yin aikin Gwamnati kafin ya shiga harkokin siyasa?

Bayan nayi hidimar kasa a Cibiyar nazarin Shuke-shuken karkashin kasa a Umudike –Umuahia a shekarar 1982-1983 na kama aikin koyarwa a Jami’ar Usman Danfodiyo dake Sokoto, a shekarar 1983-1993 na bar aikin koyarwa na kama aikin kaina na shuke-shuken itatuwa a ma aikatu na mutane masu zaman kansu daban daban. Kuma a cikin haka na samu mukamin mai bada shawara akan aikin noma da kiwo a karkashin Hukumar PTF a shekarar 1997 zuwa 1999, na kuma zama mai bada shawara a kan harkokin inganta ilmi a gwamnatin jihar Bauchi inda na rike mukamin kafa makaratun Sakandaren gwamnati na musamman kuma na yi aikin kwamitoci da yawa a karkashin gwamnatin jihar.

Na kuma yi ayyukan sa kai masu  yawa wadanda daga ciki akwai makarantar Firamari ta Millennium Academy, Tilden Fulani wadda badon neman riba ba, sai dai kawai don bada ilmi mai inganci, dakara bunkasa shi  ma al’ummar yankin Bauchi ta Kudu da jihar baki daya.

 

Ban sani ba bayan ka shiga siyasa ko ka taba rike wani mukami?

Ni ba wani mashahurin dan siyasa bane, farkon shigata harkar siyasa na yi don taimakawa janar Muhammadu Buhari ne lokacin da ya fara shiga siyasa a shekarar 2002, kamar yadda muka nemi yayi hakan, a wannan lokacin don kalubalantar Obasanjo. Ya shiga Jam’iyyar ANPP, a lokacin na bar aikina na lura da makarantu a jihar Bauchi na koma na tare a ofishinsa a Kaduna, inda muka kafa kungiyar Buhari nine Darekta na ta, na farko na bincike da dabaru, a lokacin idan ba zai samu halartar wani taro ba, na jam’iyya ni yake turawa in wakilce shi, wanda a sakamakon haka ne har Allah yasa jam’iyyar ta  tsayar da shi takarar shugabancin kasa  a  shekarar 2003 ba tare da wata hamayya ba.

 

Me nene ya saka fitowa neman takara a yanzu?

Tun a zaben shekarar 2015 mutane suke zuwa suna neman in fito takara, in sake tsayawa takara amma ganin irin magudin da aka yi mana a zaben 2003, na yi ta nokewa naki fitowa kwatsam sai Allah  yayi wa Sanata Ali Wakili rasuwa kuma wannan kira in shiga siyasa ya karu matuka a karshe Allah ne mai canja zukata Allah yasa na yarda kuma naga yanzu an gyara harkar zabe magudi ya ragu ba kamar daba.

 

To indan Allah yasa an zabe ka wadanne ayyuka zaka fara gabatarwa?

Burina shi ne inyi la’akarin da matsalolin da suka fi damun mutanen mazaba ta saboda in gabatarwa majalisa dasu,don ta taimaka mani wajen magancesu a cikin kankanen lokaci, na lura kasar mazabata tana da dausayi mai kyau da za a iya yin duk irin wani nau’i na sana’a, da mutum zai dogara dashi, ya sami rayuwa maikyau. Tana da kasar noma mai kyau tana da kasar kiwo, tana da ma’adinai duka wadannan abubuwa da Dan-Adam zai iya dogaro dasu ya sami rayuwa mai inganci, sai kuma maganar samarwa matasa aikin yi, da inganta yanayin ilmi dadai sauransu .

 

To daga karshe mene’ne sakonka ga al’ummar mazabarka?

Sakona ta wannan bangaren shine ina roko da su bani goyon baya da kuma dama in Allah ya yarada ba zanci amanarsu ba, duk wani kwabon da aka bayar don ayi wa mutane aiki ni kuma zan tabbatar da an aiwatar da aikin kamar yadda al’ummar tawa suke bukata.


Advertisement
Click to comment

labarai