Connect with us

LABARAI

Yara 500 Ne Suka Mutu Sakamakon Gubar Ma’adinai A Zamfara  –Yari

Published

on


Gwamna Abdul’aziz Yari na Jihar Zamfara ya ce, akalla yara 500 ne suka mutu sakamakon kamuwa da gubar ma’adinai a kauyaku takwas na Jihar a shekarar 2010, ba 400 ba kamar yadda aka bayar da rahoton hakan tun da farko.

Gwamna Yari, ya fadi hakan ne wajen wani taron yini biyu kan cutar ta gubar ma’adinai, wanda kungiyar masu hakar ma’adinan ta Nijeriya ta shirya a Abuja, ranar Talata.

Gwamnan wanda Sakataren gwamnatin Jihar, Farfesa Abdullahi Shikafe, ya wakilce shi, ya ce, yawancin yaran da suka kamu da cutan duk ‘yan kasa da shekaru biyar ne.

Ya ce, wasu daga cikin yaran da suka sami nasarar tsira da rayukansu suna ta fama a yanzun haka da bacewar tunanin kwakwalwarsu.

Shi dai wannan sinadarin wata guba ce wacce ake taras da ita a can karkashin kasa.

Guba ce da takan cutar da tsarin yanayin jikin dan adam, musamman ma ta fi shafan yara kanana, domin takan daskare ne a karkashin hakora da kashin jiki, da takan iya hayayyafa zuwa wani lokaci.

Gwamna Yari ya ce, ita wannan cutar ta bulla ne mako guda kafin ya karbi mulkin Jihar.

Sai ya ce, suna ganin hakan sai suka zabura da sauri, inda suka tara duk masu ruwa da tsaki kan lamarin domin tsarkake al’ummunsu daga hadarin cutar.

Ya kara da cewa, gwamnatin tarayya, ma’aikatun tarayyar da lamarin ya shafa da kungiyar likitocin kasa da kasa, duk sun kawo dauki.

Gwamna Abubakar Bello na Jihar Neja ya ce, an shirya taron ne domin a tattaro duk masu ruwa da tsaki kan lamarin domin a nuna masu mahimmancin hada kai wajen yakar cutar.

Gwamna Bello, ya yaba wa gwamnatin tarayya da sauran masu ruwa da tsakin kan goyon bayan da suka baiwa Jihar a lokacin da cutar ta barke inda har ta shafi kauyaku biyu a Jihar a shekarar 2015.

Ya ce, gwamnatin Jihar tana ta ci gaba da wayar da kan al’umma kan hanyoyin da suka dace da hakar ma’adinan, hakanan su ma masu hakar ma’adinan da ma’aikatan ma’aikatun ma’adinai, muhalli da na lafiya duk ana koya masu su ma suna koyar da hanyoyin da suka dacen da hakar ma’adinan.

Gwamna Abubakar Bagudu na Jihar Kebbi, cewa ya yi, ayyukan daidaiku masu hakar ma’adinan sun yawaita a Jihar sa ta Kebbi, ya ce, matasa da mata ne kuma duk suka mamaye aikin na hakar ma’adinan ba bisa ka’ida ba.

Gwamna Bagudu, wanda shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin na shi, Sulaiman Argungu, ya wakilce shi ya ce, Jihar Kebbi za ta ci gaba da hada kai da ma’aikatun gwamnatin tarayya wajen tsarkake masu hakan ma’adinan a Jihar, ta hanyar nuna masu hanyoyin da suka dace da aikin.

Kamfanin dillancin labarai na kasa, NAN, ya taba kawo rahoton barkewar cutar a Jihar Zamfara a shekarar 2010, inda har sama da mutane 400 suka rasa rayukan su, yawancin su kuma yara ne kanana.

Hakanan a shekarar 2016 an samu barkewar cutar a Jihar Neja, inda ta kashe mutane sama da 28 duk yara kanana.

Sai dai likitocin na kasa da kasa, sun sami nasarar dakile cutar da ta fantsama a Jihohi biyu, tare da hadin kan ma’aikatun da lamarin ya shafa da kuma gwamnatin tarayya wajen samar da kudade da kuma ma’aikata.

A kashi na farko na yakar cutar a kauyaku biyu na Jihar Zamfara, an kashe Naira milyan 150 ne, gwamnatin Jihar ce kuma ta bayar da kudaden.

A kashi na biyu kuma, a kauyaku biyar na Jihar an kashe dala milyan biyu ne domin yakar cutan, Majalisar dinkin duniya ce ta dauki nauyin shirin.

A shekarar 2016, gwamnatin tarayya ta kashe Naira milyan 250 wajen yakar cutan a kauyaku biyu na Jihar Neja.


Advertisement
Click to comment

labarai