Connect with us

LABARAI

Ranar Yaki Da Shan Miyagun Kwayoyi Ta Duniya: Gidauniyar Gyara Halayyar Matasa Ta Kaduna, Ta Kaddamar Da Kamfen

Published

on


A ranar Talata ne 26 ga watan Yuni Gidauniyar Gyara Halayyar Matasa da koya masu sana’o’i, wacce a turance ake kira da,  “Nigas Rehabilitation And Skill Ackuisition Foundation,” da ke Rigasa, Kaduna, ta kaddamar da wani gagarumin kamfen na fadakarwa da jawo hankalin matasa da ma sauran al’umma bakidaya a kan illolin da ke tattare da tu’ammuli da dukkanin abebadan da kan gusar da hankali.

An yi bikin ne don misaltuwa da ranar da majalisar dinkin duniya ta kebe musamman don yaki da wannan mummunar dabi’a ta shan kwayoyi da sauran abubuwan da kan sa maye ta duniya, wanda ya yi daidai da ranar 26 ga watan Yuni na kowace shekara. An kuma faro bikin ne tun daga cibiyar wacce aka fi sani da makarantar malam Niga da ke anguwar Rigasa Kaduna.

Da misalin karfe 8:30 na safiyar ranar ne, tawagar ta fito garin Rigasa a cikin manyan motocin kanta ta ratso babban titin da ya ratsa anguwar baki dayanta, tana tafe ana raba takardu da ke kumshe da bayanan da suka shafi dalilin shirya taron, ta biyo ta shatalentalen Nmamdi Azikwe, ta biyo titin Dutsinma, Kasuwar Barci, Kano Road Sardauna Creascent sai tawagar ta fado kan Ahmadu Bello Way, inda daganan ne aka fara tattaki da kafa har zuwa dandalin Murtala inda daman a nan ne aka shirya gabatar da jawabai.

Ba tare da bata lokaci ba, aka fara gabatar da takardu, takardar da ta fi daukan hankali a wajen taron ita ce wacce wakilin hukumar yaki da tu’ammuli da muggan kwayoyi ya gabatar. Takardar na shi ta tabo abubuwa da dama inda tun da farko ya fara bayani a kan mafiya yawan dalilan da ke sanya mutane su rika shan muggan kwayoyin, ya kuma yi bayani mai tsawo kuma mai gamsarwa a kan hanyoyin da za a iya kauce masu. Sannan ya yi bayani kan hanyoyi da kuma tsare-tsaren da hukumar na su ke bi don ganin ta raba al’umma da wannan mummunar dabi’a mai halakarwa. Wakilin hukumar kuma ya jinjina wa cibiyar ta Malam Niga musamman shugaban cibiyar da mukarrbansa a kan irin namijin kokarin da suke yi na raba ala’umma da wannan bala’in. Daga bisani ya kara jinjinawa cibiyar a bisa kokarin da ta yi na shirya wannan taron sannan ya yi kira ga sauran kungiyoyi da cibiyoyi masu zaman kansu da su yunkuro a hadu bakidaya don maganin wannan annoba kamar yadda Malam Niga ya yi.

‘Yan wasan kwaikwayo da mawaka daban-daban da kuma daliban cibiyar ta Malam Niga sun kayata wurin tare da tsuma mahalarta taron da wasanni da wake-waken da suka gabatar a wajen taron. Wanda duk suke nuni a nishadance da hadarin da ke cikin shan muggan kwayoyi.

Taron dai ya sami halarci kusan daga dukkanin matakan iko musamman na jihar Kaduna. Kadan daga cikin manyan bakin sun hada da wakilin kwamandan sojoji (GOC), wakilin shugaban ‘yan sanda na wannan shiyyar da wakilin kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Kaduna, wakilin daraktan ‘yan sandan ciki na wannan shiyyar, babban daraktan hukumar yaki da shan muggan kwayoyi na wannan shiyyar da sauransu da dama.

A karshen taron shugaban cibiyar Malam Muhammad Lawal  Yusuf  Muduru, ya gabatar da na shi dan kwarya-kwaryar jawabin, inda ya yi bayanin dalilin da ya sanya cibiyar na shi ta shirya taron, wanda ya ce an shirya taron ne don ya dace da ranar yaki da shan muggan kwayoyi ta duniya. Kuma cibiyar ta zabi ta zagaya gari ne don kara fadakar da al’umma a kan hatsarin da ke tattare da shan muggan kwayoyi. Ya kuma nu na jin dadinsa da kuma godiya ga dimbin jama’ar da suka halarci taron.

An dai yi taron lafiya, aka kuma kammala shi lafiya.

 


Advertisement
Click to comment

labarai