Connect with us

LABARAI

NARTO Ta Yabawa Buhari Kan Assasa Aikin Sabunta Hanyar Kano Zuwa Abuja

Published

on


A wani gagarimin buki mai Tarihi na kaddamar da aikin sabunta hanyar Kano, Zariya, Kaduna, zuwa Abuja, da wata tawagar wakilin shugaban kasa Muhammadu Buhari karkashin Jagorancin Ministan Aiyuka Gidaje da wutar lartarki na kasa Babatunde Raji Fashola SAN da rakiyar kananan Ministocinsa biyu Mustapha Baba Shuhuri sai Minista na uku Honorabul Sulaiman Hassan Zarma da babban Sakataren Ma’aikatar Muhammed Bukar wanda suka rufawa Minista Babatunde Fashula baya domin kaddamar da wannan aiki na sabanta da hanyar Kaduna zuwa Abuja da kuma fadadata inda kuwanne bari hagu da dama zai dau Mota hurhudu hurhudu kamar yadda Minista Sulaiman Hassan Zarma ya tabbatar a wannan Rana ta Talata da akayi Bikin budewa a Tollgate na hanyar Zariya zuwa Kaduna da ke Garin Curomawa a Jahar Kano a Arewacin Najeriya. Sai kuma gwamman jihar kaduna wanda ya samu wakilcin Hon. Hajiya Balaraba daya daga cikin kwamishinonin sa.

Haka kuma Minitan ya ce wannan aiki zai ci kudi sama da Naira Biliyan 150 inda kuma za a kamala shi cikin Shekaru uku ko kasa da haka da yardar Allah. Inda a cikin Jawabinsa Babban Minista Fashola ya ce wannan aiki da bunkasa Tattalin arzikin kasa da yaki da cin hanci da rashawa na daga cikin manyan manufofin Gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, kuma irin wadannan aiyuka na gina Hanyoyi an kammala wasu a sassa daban daban na kasan nan haka kuma ko wanna lungu da sako na Titinan Gwamnatin Tarayya za a sabantasu da kuma kirkiro sabbi a wannan gwamnati ta APC karkashin shugabancin Muhammadu Buhari.

Shikuwa daya daga cikin manyan baki masu Jawabi a wurin shugaban kungiyar NARTO masu mallakar Motocin Sifiri ta Najeriya Dakta Kasim Batayya da ya samu rakiyar shugaban NARTO na Kano Alhaji Idi Dan Fulani sun bayyana cewa wannan aiki aiki ne da zai anfani al’ummar Najeriya baki daya musamman in akayi la’akari da yadda wannan hanya ta Kano zuwa Abuja take da tasiri a harkar Sifiri a kasan nan dan haka wannan abun a yabawa shugaban kasa Muhammadu Buhari kan wannan gagarimin aiki na wannan hanya na fadadata da kuma sabanta ta a wannan lokaci da cewa abin a yaba masane.

Haka kuma Alhaji Idi Dan Fulani shugaban NARTO na Kano ya ce yana fatan sauran hanyoyin Najeriya zasu samu irin wannan aiki da aka kaddamar daga Kano zuwa Abuja inda kuma ya roki al’ummar Najeriya da a cigaba da addu’oin samun zaman lafiya da wanzuwar arziki a kasannan.

Shima Sarkin Noman Ciromawa Kano Alhaji Yusuf Nadabo Ciromawa ya bayyana wannan hanya a matsayin babban jari da taimako ga Manoman kasannan dan haka ya yabawa shugaban kasa Muhammadu Buhari akan wannan aiki haka kuma ya yabawa Mai Martaba Sarkin Malam Muhammadu Sunusi II da Takwaransa Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris wanda dukkanin su suka halarci wannan gagarimin Biki mai Tarihi inda kuma suka gabatar da Jawabinsu mai ma’ana a wannan Taro da suka halarta a Garin Ciromawa.

Taron dai ya samu halartar mataimakin Gwamnan Kano Farfesa Hafizu Abubakar wanda ya wakilci Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje wanda ya bayyana wannan aiki a matsayin kalubale ga Yan adawa kuma abun farin ciki ga al’ummar Kano da Kasa baki daya haka kuma ya yabawa Yan Jaridu da sauran al’umma wanda suka taka rawa wajan tabbatar wannan aiki. Shima Hon. Mustapha Abdullahi Rabi’u Kura shugaban karamar Hukumar Kura ya ce suna sahun gaba wajan cin gajiyar wannan aiki kuma irin wannan aiyuka na cigaban kasa Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ke shimfidawa Kano.

 


Advertisement
Click to comment

labarai