Connect with us

LABARAI

Annobar Guguwar Bauchi:  Kungiyar Masu Maganin Gargajiya Ta Bukaci Kafa Gidauniya Domin Bayar Da Tallafi

Published

on


Kungiyar masu sarrafawa da tace magungunan gargajiya ta jihar Bauchi ta bukaci gwamnatin jihar da ta kafa wata gidauniya domin tallafawa wadanda waki’ar iskar ruwan sama ta shafa.

Shugaban kungiyar ta jihar, Dakta Gambo Abdullahi Bababa wanda ya gabatar da wannan bukata, ya kuma mika jajen kungiyar ga wadanda waki’ar ta shafa, yana mai addu’ar Allah ya basu hakurin cin wannan jarrabawa.

“Abin bakin cikine, kuma abin tausayawa ne ga ‘yan-uwa da suka shiga cikin wannan masifa. Wasu gidajensu sun rushe, wasu ma sun rasa rayukansu musabbabin wannan waki’a,” In ji Bababa

Shugaban, wanda ya roki Allah Subahanahu Wata’ala ya kawo sanadiyyar mayar da wadannan gurabai na asarori da jama’a suka yi sakamakon iskar, yana mai fatar Allah ya yaye masu radadin wannan masifa.

Bababa ya kuma yi kira ga gwamnatin jihar da ta gaggauta taimakawa wadanda waki’ar ta shafa domin nuna tausayi kan halin da suka samu kansu a ciki.

Dakta Gambo Bababa ya kuma yi kira ga masu hannu da shuni, da masu arzikin tallafawa dasu kawo agaji ga wadannan bayin Allah domin neman yardar Ubangiji Mahalicci.

Ya ce, babban kiransa zai tafi ne wa gwamnatin tarayya, wacce ya ce ita take da babbar rawar takawa kan wannan lamari wajen jinkai ga wadanda waki’ar ta akkawa.

“Ya zama wajibi wa gwamnatin tarayya ta kafa wani kwamiti wanda zai kunshi nagartattun mutane, ba wadanda zasu sa rigar addini domin su cuci jama’a ba wajen rabon kayayyakin tallafi da kudade wa wadanda waki’ar ta shafa ba”.

“Yanzu haka a jihar Bauchi sanadiyyar wannan waki’ar ta iska an rasa gidaje sunfi dubu daya, an rasa rayuka sun fi talatin a nan cikin garin Bauchi, wannan ba karamar masifa bace”, kamar yadda ya misalta.

Ya bukaci gwamnati ta kafa kwamiti wacce za ta kunshi mutane masu tsoron Allah, ba wadanda zasu ambaci Allah a baki baije makogoro ba, masu amfani da addini suna cutar jama’a ba.

Ya yi la’akari da da cewar, wannan waki’a wani al’amari ne daga Allah, wanda idan an kwatanta bai kai sukusin da wadansu al’umman duniya suka samu kansu ciki ba, sai dai kamar yadda ya fadi, abin da ya shafi mutum shine yake dubawa kuma shine yake gani.

Dakta Bababa ya yi fatar kada Allah ya sake jarrabar jama’ar Bauchi, Nijeriya dama duniya baki daya da irin wannan masifar wacce jama’ar Bauchi basu taba ganin irinta ba, sannan sai ya yi kira ga jama’a dasu dukufa yin istigifari ga Allah tare da neman gafararsa.

“Allah ya jikan wadanda suka rigamu gidan gaskiya sanadiyyar wannan waki’a, Allah ya yaye mana wannan hali da muke ciki, kuma mu gyara halayyar mu, kowa ya san matsalar da take akwai tsakaninsa da Ubangijinsa, ba sai an gaya masa ba, muji tsoron Allah koya jikanmu ya tsausaya mana ba don halinmu ba” In ji Gambo Bababa.

 


Advertisement
Click to comment

labarai