Connect with us

LABARAI

An Bukaci A Kawo Wa Sashin Ilimin Kasar Nan Dauki

Published

on


An bayyana cewa, lokaci ya yi da ya kamata al’umma su hada hannu domin taimaka wa harkokin ilimi a fadin kasar nan musamman a arewaci da aka bar al’umma a baya ta fannin samar masu da ilimi mai kyau da inganci idan ka kwatanta da na kudancin kasar nan .

Wannan bayani ya fito ne daga bakin shugaban cibiyar na’ura mai kwakwalwa da ake kira MSK Computer Institute dake kan hanyar Air Port Road a Kano, Muhammed Suleiman Kano a lokacin da yake zantawa da manema labarai kwanakin baya a ofishinsa ciki har da Leadership A Yau.

Muhammed Suleiman ya ce kamar yadda gwanatoci ke bakin kokarinsu domin ganin harkokin ilimi sun inganta soboda haka ya zama wajibi masu hali suma su kara azama a kan taimakawa ilimin, shugaban cibiyar ta MSK Computer Institute ya ce hatta wadanda ba su da hali suma suna da rawar da za su taka domin bayar da ta su gudunmawar wajen taimakawa ilimin.

Daga na sai ya jawo hankulan malamai dake karantarwa a makarantun kasar nan da cewa su sanya tsoron Allah da kwatanta gaskiya da kuma karantar da dalibai tsakani ga Allah ba tare da son zuciya ba. Su kuma dalibai su zamanto masu da’a da biyayya ga malamai tare da mayar da hankali a kan abin da ake karantar da su, tare da kaucewa duk wani abu da zai kawowa karatunsu nakasu su tabbatar sun tambayi malami a kan abin da ba su fahimta ba domin karin bayani.

Har ila yau su rika zuwa makaranta a kan lokaci domin zuwa makaranta ga dalibi yana da muhimmanci. Da ya juya ga iyayen yara kuwa Malam Muhammed Suleiman Kano, ya hore su da su rika tabbatar da cewa, ‘ya’yan na su suna zuwa makaranta, tare kuma da yawaita kai ziyara makarantun su da kuma duba littafansu domin ta haka ne za su iya fahimtar cewa suna zuwa makaranta ko ba sa zuwa.

Ya kuma ce cibiyar ta shi ta MSK Computer Institute a shirye take ta ci gaba da bayar da gudunmawa wajen inganta harkokin ilimi a jihar Kano da kasa baki daya da yardar Allah musamman akan abin da ya shafi jarabawa ga dalibai. Babbar abin da MSK ke bukata shi ne addu’oin fatan alhairi ga al’ummar jihar Kano da kasar nan baki daya .

Daga karshe ya taya daukacin al’ummar musulmi murnar kammala watan Azumin Ramadan lafiya da fatan Allah ya baiwa jihar Kano da kasar nan zaman lafiya da karuwar arziki


Advertisement
Click to comment

labarai