Connect with us

LABARAI

Nijeriya Ta Zarce Indiya A DuniyaNijeriya Ta Zarce Indiya A Duniya

Published

on


Rahotannin daga “Brookings Institution” sun nuna cewa halin yanzu, Nijeriya ce qasar data tattara mutanen da suke fuskantar matsananciyar talauci a duniya. Kafin yanzu qasar Indiya ce ke riqe da wannan kanbun, qasar da ke da yawan jama’ar da suka kai Biliyan 1.324, yayin da Nijeriya ke da jama’ar da suka kai Miliyan 200.
Rahoton ya nuna cewa, mutanen dake fuskantar matsanancin talauci na qaruwa da mutum 6 a cikin kowanne minti xaya.
“Kamar yadda bincikenmu ya nuna, tuni Nijeriya tayi wa qasar Indiya fintinkau wajen yawan mutanen dake fuskantar tsananin talauci a shekarar 2018, yayin da qasar Kongo ke a matsayin mataki na 2”
“A qarshen watan Mayu na shekarar 2018, hashashenmu ya nuna cewa, Nijeriya nada mutum fiye da Miliyan 87 da suke fuskantar matsanancin talauci, hakan kuma yana qaruwa ne da misalin mutum 6 a cikin kowanne minti xaya, yayin da lamarin ke qara sauka qasa Indiya
Gaba xaya lamarin zai kasance kafin qarshen shekarar 2018 za a samu qarin mutum Miliyan 3.2 da za su faxa cikin matsanancin talauci a yankin Afrika fiye da abin da muke da shi a halin yanzu.”
“Yan Afrika sune kusan kashi uku na masu fuskantar matsanancin talauci a duniya, in har kuma ba a yi wani abu ba, lamarin zai iya ninkawa nan da shekarar 2030.
“Qasashe 18 daga cikin qasashen da matsanancin talauci ke bunqasa a halin yanzu suna a cikin qasashe Afrika ne.”
A watan Maris data gabata hukumar Lamuni ta Duniya (IMF) ta bayyana cewa, ‘yan Nijeriya na ci gaba da qara talaucewa, saboda haka ta buqaci a fito da wasu matakai da zai taimaka wajen bunqasa tattalin arrziqin qasa.


Advertisement
Click to comment

labarai