Connect with us

LABARAI

Kashe-kashe: Osinbajo Ya Ziyarci Filato, Ya Yi Alkawarin Hukunta masu Hannu A Harin

Published

on

A ranar Litinin ne mataimakin shugaban kasa Yemi Osibanjo, ya ziyarci jihar Filato bayan aukuwar rikice rikicen da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.
Idan za a iya tunawa fiye da mutane 80 aka hallaka a cikin kwanaki 2 a hare haren da aka kai wasu sassan jihar Filato.
Mista Osibanjo, wanda ya je jihar ne don nazarin yadda lamarin rikicin ya kasance ya kuma tattauna da shugabannin al’umma inda ya yi alkawarin cewa, lallai za a kama tare da hukunta duk wanda ke da hannu a ta’addacin da aka tafka, ya ce, tuni aka tura runduna na musamman don tabbatar da zaman lafiya a jihar.
“Shugaban rundunar ‘yan sanda ya karo dakarunsa jihar filato, rundunar sojojin Nijeriya ta kuma sanar da sassafen nan cewa, za a samar da rnduna na musamman don dawo da zaman lafiya jihar Filato baki daya.
“Rundunonin nan musamman za su hada hannun ne da rundunar “Operation Safe Haben” don tabbatarbda zaman lafiya a sassan jihar ta Filato,” inji shi.
Mataimakin shugaban kasan ya kuma nuna bacin ransa dangane da faruwar wannan ta’addancin.
“Shugaban kasa ya ce a sanarwarsa, dukk wanda ked a hannu a wannan ta’asar za a tabbatar da an kama tare da hukunta shi,” inji shi.
Ya ce, gwamnatin tarayya bata ji dadin faruwar wannan lamarin ba, saboda jihar Filato ta zama kamar wani sampuri na yadda ake samar da zaman lafiya kafin aukuwar wannan lamarin.
Mista Osibanjo ya kuma bukaci dukkan shugabannin yankin su yi taka tsantsan da abin da zasu furta da kuma aiyyukansu a dai dai wannan lokacin domin kaucewa ci gaba da habbakar riicin.
A nasa jawabin, gwamnan jihari Filato Simon Lalong, ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan da suka rasa rayuka da dukiyoyin ‘yan uwansu.
Mista Lalong ya ce, lamarin ya bata masa rai ne musamman ganin cewa, a lokacin daya zama gwamna kabilar Biron dana Fulani sun sanya hannu a kan wani yarjejeniyar zaman lafiya da juna tare da kuma tsara hanyoyin dauna lafiya da juna.
Ya kara da cewa, a halin yanzu wasu daga cikin shawarwarin da aka cimma ana shirye shiryen zama dasu doka. Ya kuma mika godiyarsa ga gwamnatin tarayya a bisa gagauta kawo dauki da tayi don ganin an dakile rikicin.

Advertisement
Click to comment

labarai