Connect with us

LABARAI

Gwamnatin Katsina Ta Yi Alkawarin Daukar Nauyin ’Yan Gudun Hijira A Jihar Katsina

Published

on


Gwamnatin jihar Katsina ta bada tabbacin na kawo dauki ga yan gudun hijira na cikin gida da suka gudo daga jihar Zamfara da suke zaune a Dansabau dake karamar hukumar Kankara.
Gwamna Aminu Bello Masari ya bada tabbacin a lokacin da ya ziyarcesu tare da sakataren gwamnatin jihar Katsina Alh. Mustapha Mohd Inuwa don jajanta masu.
Gwamnan ya ce daya daga cikin nauyin dake kan shugabanni shi ne su samar da sauki ga jama’a tare da gano mabukata don a taimaka masu.
Ya bada tabbacin cewa gwamnatin zatayi abinda ya kamata don taimakon yan gudun hijirar wanda da damarsu daga goyon gangama suke ne jihar Zamfara.
Ya ce al’ummar Dansabau na bukatar addu’a da yabo saboda nuna kokari ta hanyar karbar bakuncin yan gudun hijirar dake jihar Zamfara.
Alh. Aminu Bello Masari ya ce kafin karshen wannan shekara za’a kammala hanyar Kankara-Zango-Dansabau kuma gwamnati zata duba yiyuwar yin hakan domin ganin an samu saukin irin wadannan bala’o’i dake addabar jama’a kamar yadda ya kamata gwamna Aminu Bello Masari ya yabama mutanen kauyen Dansabau bisa irin tausayi da suka nunama yan udun hijira bayan nan gwamnan yayi alkawarin duba matsalolin bakin iya gwargwado domin taimaka masu da nufin kowannensu ya koma gidansu ba tare da wani fargaba ba.


Advertisement
Click to comment

labarai