Connect with us

LABARAI

Filato: Rayukan ’Yan Nijeriya Sun Zama Kamar Gyada -Shehu Sani

Published

on


Dan Majalisar Dattawa mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Kwamared Shehu Sani ya ce, rikicin da aka yi fama da shi kwanan nan a Jihar Filato wanda ya yi sanadiyyar rasa rayuka 80 da lalata gidaje 50, daya ne daga cikin makamantansa masu yawa.
Shehu Sani, ya fadi hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin a Abuja, ya bayyana lamarin da cewa, abin takaici ne da bakin ciki, a ce kullum sai kashe mutane ake ta yi a Nijeriya.
Ya nu na damuwarsa kan yadda a daidai lokacin da ake ta halaka ‘yan Nijeriya, su kuma ‘yan siyasar kasar hankalinsu yana wajen neman mulki ne a zaben 2019.
“Daidai lokacin da gwamnoni suke rawa suna juyi, annashuwa da wake-wake suna ta sheke ayarsu a dandalin, Eagle Skuare, talakawansu kuma suna can ana ta kashe su ne.
“Gaskiyan lamari shi ne, yau a Nijeriya, ran talaka ya fi gyada da Gala arha.
“Mun zama kasar da a kullum muke cikin juyayin rashe-rashe da jana’iza.
“An zubar da jini mai yawa a Nijeriya da ya kamata a ce ya sosa rayukan duk wani mai mulkin da ya san abin da yake yi, amma fa sai in yana da tausayi irn na dan adam a tare da shi.
“Matukar dai ‘yan siyasar da ke kan mulki ba za su rika ganin kimar rayukan raunana talakawansu daidai da nasu su kansu ba, to kuwa ba ranar da za a daina shekar da jinainan talakawa a kasarnan.
“Kasa ta rasa sanin kimar ayyukan assha da ake ta tafkawa, a kullum sai tarba, kada ganguna da yabon shugabannin da suka kasa sauke nauyin da ya hau kansu suke,” duk in ji Sanata Shehu Sani.
Daga nan sai ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan, ya kuma yi rokon Allah Ya rahamshe su.
Rundunar ‘yan sandan Jihar ta Filato ta tabbatar da kisan mutane 86 a hare-haren da aka kai a kauyakun Razat, Ruku, Nyarr, Kura da Gana-Ropp, duk a yankin Gashish ta karamar hukumar Barkin Ladi.


Advertisement
Click to comment

labarai