Connect with us

LABARAI

ASUU Ta Nuna Damuwarta Kan Yawaitan Jami’o’i A Nijeriya

Published

on


Duk da yadda ake ta yawan kafa Jami’o’i a kasarnan, har yanzun ba a iya daukaka martaba da kimar wadanda ake da su ba, kungiyar malaman Jami’o’i ta kasa ASUU, reshen Jami’ar Jihar Legas ce ta fadi hakan.
Shugaban kungiyar, Dele Ashiru, ya yi nu ni da cewa, ga dai Jami’o’i masu yawa a kasarnan, amma dai yawan na su bai iya bayar da sakamakon da ake da bukata ba.
“Yanzun ka ji an ce an kafa sabuwar Jami’a, ba tare da jin wani kyakkyawan sakamako da na da da ake da su suka bayar ba, a fannin siyasa ne ko zamantakewa ko kuma bunkasa tattalin arzikin kasa.
“Ina bugun kirjin cewa, rashin takaita yadda sabbin Jami’o’in ke ta kunno kai a kasarnan, a gaskiya, shi ne daya daga cikin dalilan da ya sanya tsarin ba ya iya haifar da wani da mai ido.
“Yawancin ma Jami’o’in ba su da isassun ma’aikata, musamman malamai masu koyarwa, ballantana ma a yi maganan kayan aikin da suka dace su samar da lafiyayyen ilimi.”
Mista Ashiru ya ce, akwai bukatar a yi gaggawan tallafan Jami’o’in da muke da su a halin yanzun, na gwamnati ne ko masu zaman kansu, a samar masu da kayan aikin da suka dace, domin su iya fuskantar kalubalen da ke fuskantar kasannan.
Shugaban kungiyar ya ce, kara kirkro Jami’o’in ba shi ne mafita ba ga matsalar ilimin kasarnan da sauran kalubalen da ke fuskantar tsarin ilimin kasarnan bakidayansa.
Ya ce, maimakon a yi ta kafa sabbin Jami’o’i, kamata ya yi a karfafi wadanda ake da su a halin yanzun ta yadda za su kasance masu amfani wajen samar da ci gaban kasarnan.
A cewar shi, ya wajaba a yi wani abu mai karfi da zai samar da yanayi mai kyau a Jami’o’in da zai janyo hankali tare da tabbatar da masanan da muke da su a Jami’o’in namu, da suka hada har da masana daga wajen kasarnan.
Mista Ashiru ya ce, “Sam ba ma son ‘yan siyasa ko mutanan da suka gaza a fannin ayyukan banki suka kuma rasa wani aikin yi, su zo suna more wa rashin isassun malaman da muke da su a Jami’o’in namu.
“Koyarwa a Jami’a abu ne na wanda ya sami horo a kan hakan, matukar ba ka da horon hakan, ba wani abin kirkin da za ka iya tsinanawa.
“Jami’a kuma ba fage ne na siyasa ba, ba wuri ne da mutane za su zo suna yin siyasa ba, kamar yanda muke ganin hakan na faruwa a wasu Jami’o’in namu.”
Shugaban kungiyar kuma ya nu na damuwarsa kan wasu Jami’o’in masu zaman kansu da aka kafa su domin neman riba, wadanda a kullum suke fadi tashin lallabar Majalisun kasa da su yi gyara a dokar samar da kudade domin su ma su rika samun tallafi daga gwamnati.
A karshe sai ya bukaci hukumar da ke kula da Jami’o’in, NUC, da su kara tsaurara matakan kafa sabbin Jami’o’in ta kuma tabbatar da wadanda ma ake da su a halin yanzun sun cika ka’idojin da aka tanada.


Advertisement
Click to comment

labarai