Connect with us

LABARAI

Ana Sa-In-Sa Da Xaliban Jami’ar Wudil Kan Tara

Published

on

An shiga sa-in-sa tsakanin hukumar gudanarwa ta Jami’ar Kimiyya da fasaha ta garin Wudil da xalibanta tun bayan sanarda ranarda za’a sake buxe jami’ar da sanya musu tarar kuxi N17,000 ga kowane xalibi.
Hukumar jami’ar ta bayar da sanarwar sanya ranar Litinin 9 ga watan Yuli xalibai su koma jami’ar bayan rufeta da akayi kwanakin baya dalilin zanga-zangar data jawo fashe-fashen muhimman wasu kayayyaki da gine-gine a harabar jami’ar saboda mutuwar wani xalibi a kogin wudil.
Sai dai tararda jami’ar ta gindaya ga kowane xalibi na zunzurutun kuxi N17,000 tasa xaliban sun nuna rashin gamsuwarsu duba da halinda ake ciki na matsi wanda da yawa da kyar ma suke iya gudanarda karatun nasu a daddafe.
Irin wannan kokawa da xaliban suka yi, sai suka sake tunzura hukumar jami’ar da suka kirawo taron manema labarai inda mataimakin shugaban jami’ar Farfesa Shehu Musa Alhaji ya bada sanarwar rushe kungiyar xalibai na jami’ar bisa zarginsu da gazawa wajen jagoranci da kuma nanata dalilansu na sanya tarar ga dukkan xaliban jami’ar.
Farfesa Shehu Musa Alhaji a yayin zanga-zangarda xaliban suka yi ran 2 ga watan mayu na shekararnan sun lalata kayayyaki a wurare 21 cikin jami’ar ciki harda matar xaukar marasa lafiya da kuxinta yakai N40,000,000.
Ya kara da cewa an rushe kungiyar xalibanne saboda dalili na tabbatarda tsaro dan cigaban jami’ar tareda umurtar kungiyar ta mika duk wasu kayyayaki ga hukumar jami’ar.
Sai a nasu bangaren xaliban basu amince da rusa kungiyarba tareda cewa jami’ar bata xauki mataki na adalci ba suna ganin Jami’ar ta xauki matakin rusa kungiyarne saboda taki bada haxin kai wajen a kakabawa xalibai tararda suke ganin wasu yan tsirarune suka aikata laifin.
Sun bayyana cewa suna nan akan shugabancin kungiyar da xalibai ne suka kafata ba,kuma zasu cigaba da fafutukar ganin an sassauta tarar.
Wata xaliba ta ce ko a ranar da a ka yi zanga-zangar ba xaliba ko xaya mace a ciki, sannan kuma yawancin xaliban ma da kyar suke iya biyan kuxin rijistar jami’ar a halin da ake ciki na matsi.

Advertisement
Click to comment

labarai