Connect with us

LABARAI

An Tura Sabon Kwamishinan ’Yan Sanda Filato Domin Dakile Kashe-kashe

Published

on


Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta aike da sabon Kwamishinan ‘yan sanda zuwa jihar Filato bayan tashin-tashin da aka yi ta samu wanda ya yi sanadiyyar mutuwar rayukan jama’a da dama a kauyukan da suke karamar hukumar Barkin Ladi da ke jihar Filato.
Bala Ciroma dai ya kasance mataimakin Kwamsihinan ‘yan sanda ne mai kula da sashin bincike da sashin aiki da kaifin basira wato (CIID) a babban birnin tarayya FCT Abuja inda ya kama aiki a matsayin kwamishinan Jihar Filato a jiya Talata.
A cikin wata kwafin sanarwar manema labaru daga jami’in hulda da jama’a na rundunar ASP Tyopeb Terna ya shaida cewar Bala Ciroma ya kasance jami’in dan sanda da yayi aiyuka a fannoni daban-daban inda kuma ya yi aiki a yankunan kasar nan daban-daban, inda aka shaida cewar yana da kwarewa kan wasu ababe da daman gaske.
Ya shaida cewar sabon kwamishinan an haifesa ne a jihar Yobe, inda ya yi karatunsa a jami’ar Maiduguri ya kai ga kammalawa ne a shekara ta 1988, inda kuma ya fara aikin dan sanda da mukamin mukaddashin sifiritandan a ranar 3 ga watan Mayu 1990.
ASP Terna ya ce; “Ya yi aikin dan sanda a wurare daban-daban a fadin kasar nan, ya kuma taka mukamai daban-daban a aikin dan sanda a fadin kasar nan,” In ji sanarwa.
Wakilinmu ya labarto cewar sabon kwamishinan CP Bala Cirooma shine ya maye gurbin Kwamshina Andie Undie wanda aka turasa aiki jihar Filato a watan Satumban 2017, wanda kuma aka amshi kujerar tasa a ranar 26 ga watan 6, 29018.


Advertisement
Click to comment

labarai