Connect with us

LABARAI

An Cafke ’Yan Nijeriya Shida Da Laifin Damfarar Kamfanin Amurka

Published

on


Hukumomin tsaron Nijeriya sun ce an damke ‘yan Nijeriya 6 a bisa hannunsu a wata badakalar damfara tsakanin yankin Afrika da kasar Amurka inda suka yi awon gaba da miliyoyin daloli na kanfanonin ‘yan kasar Amurka.
Biyar daga cikin wadanda ake zargin sun hada da mutum daya dan kasar Mekzico da mutum 2 ‘yan Amurka da dan kasar Gana da dan kasar Nijeriya 1, an kuma kama su ne a kasar Amurka, kamar yadda ma’aikatar shari’ar Amurka ta bayyana.
Sauran 3 kuma, 2 ‘yan kasar Gana da dan Nijeriya 1 an kama su ne a wajen kasar Amurka, ana kuma nan ana shirin shigo dasu Amurka don su fuskanci shari’a.
Wannan kamen ya zo ne a kokarin ma’aikatar shari’ar amurka na katse zirga zirgan sakonnin kudade na damfara da sunan kasuwanci da ake yi da kanfanoni da daidaikun mutane a kasar Amurka, inda aka kiyasta danfara kudi fiye da Dala Miliyan 15.” Inji mai rike da mukamin Ministan Shari’a, John Cronan.
Wadannan kamun yana kuma cikin wani yukuri da gwamnatin Amurka da kuma hadin gwiwar rundunonin tsaro na kasashen duniya ke jagoranta, shirin da suka sanya wa suna “Operation Keyboard Warrior” don katse hanzarin masu danfara ta intanet dake kai hari Amurka daga kasashen Afrika.
Masu dada baki a harkar damfarar daga kasashen Afrika sun dade suka tafka wadannan ta’asar ta hanyar amfani sa sakonnin email da sauran hanyoyin sadarwar intanet tun daga shekarar 2017, kamar dai yadda takardar zargin ya nuna.
Masu damfarar na mafani da adireshin email ne wajen samun cikkaken bayanan mutum, suna kuma amfani da bayanan don su fahinci yanayin huldar kudade da mutumin ke yi, daga nan sais u shiga aika masa sakonnin email da nufin neman shiga harkar kasuwanci da shi daga nan ne sai a damfare shi.
Ana kuma zargin wasu daga cikin ‘yan Afrikan da shiga soyayar karya da nufin damfara da kuma yaudara da suna cinikin gwal da sauransu.


Advertisement
Click to comment

labarai