Connect with us

LABARAI

Amurka Ta Yi Tir Da Kashe Kashen Jihar Filato

Published

on


Kasar Amurka ta yi tir da kashe kashen daya auku a jihar Filato inda aka kashe fiye da mutum 86 yayin da wasu da dama suka ji munanan raunuka.
A sanarwa da Amurka ta bayar ta hannu jami’ar watsa labaranta Misis Heather Nauert, ta ce, dole a a tabbatar da hukunta masu hannu a ta’asar da aka tafka.
“Kasar Amurka ta yi kakkausar Allah wadai kashe kashen fararen hula da kuma barnatar da dukiyoyin jama’a da aka yi a yankin tsakiyar Nijeriya a karshen makon daya gabata.
“Mun damu matuka da karuwar tayar da hankula da kuma amfani da makamai, muna kuma kira ga jagororin siyasa dana al’umma su hada hannu wajen ganin an samu kawo karshe rikice rikicen daya addabi yankunan karkarar tsakiyar Nijeriya da nufin kawo zaman lafiya mai dorewa.
“Muna tare da shugaba Muhammadu Buhari wajen aikawa da sakon ta’aziyyarmu ga al’ummun da wannna lamarin ya shafa, nuna kuma fatan za a tabbatar da hukunta duk wanda aka samu da hannu domin ganin hakan ya yi maganin sake aukuwar irin wannan a nan gaba.” inji Nauert.
Jami’in watsa labaran rundunar ‘yan sanda jihar Filato, ya tabbatar da cewa, makiyaya sun kona gidaje 50 da motoci 2 da kuma mashina 15.
Bayani ya nuna cewa, makiyayan sun mamaye kauyukan Razat da Ruku da Nyarr da Kura da kuma kauyen Gana-Ropp da suke yankin Gashish na karamar hukumar Barkin Ladi inda aka samu kashe-kashe mafi yawa.
Tuni gamnatin jihar Filato ta kakaba dokar hana fita a yankin Riyom, dake kananan hukumomin Barkin Ladi dana Jos ta Kudu, bayan da kashe kashen ya yi kamari. Shugaba Muhammadu Buhari ya yi tir da harin da aka kai, ya kuma yi alkawarin hukunta duk wani mai hannu a kashe kashen da aka yi.


Advertisement
Click to comment

labarai