Connect with us

LABARAI

NURTW Za Ta Dakatar Da Duk Direban Da Ta Samu Da Laifin Shaye-shaye –Bala

Published

on


An bayyana cewar duk a cikin kungiyoyin sufuri a Najeriya NURTW kadai ce kungiyar sufuri da ke sayarwa kasar nan kudin haraji bisa ka’ida, domin duk rasitan da muke anfani da shi hukumar buga tikiti ta kasa ce ke bugawa. Shugaban kungiyar sufuri ta NURTW reshen jihar Neja, Alhaji Garba Musa Bala ya bayyana hakan ga manema labarai a Minna.
Alhaji Bala ya cigaba da cewar a kungiyan ce bisa tsari duk direban da ya samu matsala indai mamban mu ne, kungiya ke daukar dawainiyar yawancin matsalolin, don haka muna tsaurarawa sosai, dan gane da halin shaye-shaye da ya zama ruwan dare yanzu duk direban da muka samu da laifin shaye-shaye koda kuwa motar wa yake tukawa mu kan kwace motar a hannun sa, domin NURTW ta da rayuwar fasinja fiye da komai, dukkanin garejin da ake lodi kofa a bude ta ke ga duk fasinjan da aka yi mai ba daidai ba da ya kai kokensa mu kuma da zaran mun bincika mun tabbatar da gaskiyar lamari za mu dauki mataki ba tare da bata lokaci ba.
Dangane da lodin fasinja da kaya da direbobin kan yi da ke wuce kima, shugaban yace ba laifin kungiyar mu ba ne, laifi ne na jami’an kare hadurra ta kasa da jami’an kula da motoci akan hanya. Da suna aikinsu yadda ya kamata da duk ire-iren wadannan laifukan da sun yi sauki, mu a garejin akwai adadin kayan da muka amince direba ya dauka, kuma ba direban da zai laifi mu goyi bayan sa, don haka wajibi ne hukumomin da alhakin ya rataya a wuyansu su mayar da hankali akan nauyin da ya rataya akansu.
Yau NURTW tana da shekaru arba’in tana aikin sufuri a kasar nan, in ko sanin doka ne ba na tunanin akwai wata kungiya da ta fita sanin dokar hanya, da yake yanzu lokacin siyasa ne kungiyoyin sufuri na ta fitowa da dama wadanda wasu ba hakkin fasinja ba ko na direba ba sa iya karewa, da jami’an da alhakin kula da hanya da tuki gami da lafiyar mota na aikinsu yadda ya kamata da an samu saukin hadurra a kasar nan.
Shugaban ya tado batun lalacewar hanyoyin kasar nan, yace maganar gaskiya aikin ba na rana daya ba ne domin da gwamnatocin da suka gabata suna kokartawa kamar yadda gwamnatin ke yi yanzu ina da tabbaci da mun yi nisa, kusan duk ayyukan da gwamnatin nan ta gada na aikin hanya koda tazo matsalolin da ta iske akansu ya wuce abin magana, amma duk da hakan tana bakin kokarinta dan duk mai bin hanyar Suleja zuwa Minna ya ga inda aka dosa, amma duk da haka muna jawo hankalinta gwamnati da ta kara himma domin hanya ce ta inganta tattalin arzikin kasa.
Alhaji Bala ya jawo hankalin direbobi akan bin doka da oda kan haka ne yasa lokaci lokacin NURTW ta samar da lokutta dan wayar da kan direbobi ta kiran shugabannin shiyya dan shirya masu tarukan karawa juna sani, kuma ya kamata jama’a su sani musamman masu hawar motocin sufuri akan hanya, yace akwai hatsari sosai dan ta nan ne ake hawar motocin bata gari, wanda wani lokacin akan fada hannun masu garkuwa da mutane ko kuma ‘yan fashi.


Advertisement
Click to comment

labarai