Connect with us

LABARAI

Kashe-kashen Filato Abin Takaici Ne –Buhari

Published

on


Shugaba Muhammadu Buhari ya nu na bakin cikinsa kan samun labarin kashe-kashen da aka yi wa mutanan da ba su ji ba, ba su gani ba, a Jihar Filato, ya kuma sha alwashin gwamnatinsa ba za ta gaza ba, har sai an kamo wadanda suka yi wannan danyan aikin da masu daukan nauyin su.
Shugaban ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twita mai adireshin; @MBuhari, a daren ranar Lahadi a Abuja.
Ya kuma mika ta’aziyyarsa ga al’ummu da iyalan wadanda abin ya shafa.
Sakon Shugaban kasan a shafin na shi na Twita cewa yake yi, “Kisan rashin imani da lalata dukiyoyin da aka yi a Jihar Filato abin ba dadi, kuma abin takaici ne.
Rundunar ‘yan sandan Jihar ta Filato ta tabbatar da kisan mutane 86 a hare-haren da aka kai a kauyakun Razat, Ruku, Nyarr, Kura da Gana-Ropp, duk a yankin Gashish ta karamar hukumar Barkin Ladi.
Tun da farko dai, rundunar cewa ta yi mutane 11 ne aka kashe.
Kakakin rundunar Jihar, Terna Tyopeb, shi ya tabbatar da sabon lissafin a ranar Lahadi a Jos.
Terna Tyopeb, ya ce, “Sakamakon harin da aka kai a gundumar Gashish, ta Barikin Ladi, Kwamishinan ‘yan sanda, Mista Undie Adie, ya tura dakaru yankin domin su yi aikin ceto su kuma gano hakikanin barnar da aka yi.
“Bayan sun yi bincike da kyau a kauyakun da aka kai harin, sun gano mutane 86 da aka kashe, da kuma wasu shida da aka raunata.
“Gidaje 50, motoci 2, da babura 15 duk an kone su.”
Tuni dai gwamnatin Jihar ta sanya dokar tabaci daga karfe shida na yamma zuwa shida na safiya a Riyom, Barikin Ladi, da karamar hukumar Jos ta kudu, domin gujewa bacin bin doka a Jihar.


Advertisement
Click to comment

labarai