Connect with us

LABARAI

Farfesa Malami Ya Bukaci A Tallafa Wa Wadanda Ibtila’i Ya Shafa A Bauchi

Published

on


Daya daga cikin ‘yan takarar kujerar gwamnan jihar Bauchi a zaben 2019 da ke tafe Farfesa Sani Abubakar Malami ya mika sakon ta’aziyyarsa da kuma jajensa ga wadanda ibtila’in Guguwa da Gobara ta shafa a jihar Bauchi.
Farfesa Malami wanda ya yi jajen nasa a lokacin da ke zantawa da wakilanmu a Bauchi, ya shaida cewar wadanda matsalar ta shafa suna gayar bukatar tallafin masu hanu da kumbar susa, yana mai kiran gwamnatin jihar Bauchi da ta tashi tsaye domin taimaka wa wadanda lamarin ya shafa kai tsaye.
Malami wanda yake neman kujerar gwamna a karkashin jam’iyyar GPN ya nuna damuwarsa kan halin da jama’a suka shiga, yana mai addu’ar Allah kare aukuwar hakan gaba.
Ya ce; “Ina mai mika sakon ta’aziyyata ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu a sakamakon barnar da Guguwar ta yi a Bauchi, Allah ya jikansu ya kuma sanya mutu ta zama hutu a garesu.
“Ina mai kuma jajanta wa dukkanin wadanda abun ya shafa tun daga garin Azare wanda Gobara ta gona kasuwar gari baki daya da lakumi miliyoyin naira, da kuma jama’an da Guguwa ta yi wa barna a Bauchi da kewa wanda aka yi asaran dukiyoyi da muhallai, ina mai jajantawa da kuma fatan Allah ya maida abun da ya fi abun da aka rasa da alkairinsa,” A cewar Farfesa Malami.
Ya ci gaba da jawabinsa da cewa; “Baya ga wannan jajen nawa, ina kuma kira ga masu hanu da shuni da su shigo su taimaka a yi aikin sadaka a taimaka wa wadanda wannan lamarin ta shafa, koda da kosa daya ne ka taimaka wa mutum ka taimaka masa, muna kira ga masu hanu da shuni su taimaka,” In ji Malami.
Ya kuma shaida kiransa ga gwamnati domin kara samar da tallafi wa jama’a, “shugaban kasar Nijeriya ya zo ya yi mana jaje, gwamnan jihar Bauchi shi ma ya yi mana jaje. Mun ga matakin da hukumar samar da agajin gaggawa ta kasa SEMA ta fara dauka; don haka muna kira ga gwamnatin jiha da ita ma ta fara daukan matakan tallafi da suka dace. Domin labarin da muke samu wai za a yi kwamiti da zata taimaka amma mu dai bamu ga komai a kasa ba, don haka muna kiran gwamnatin jiha ta taimaka wa wadanda wannan ibtila’in ta shafa,” In ji Shi.


Advertisement
Click to comment

labarai