Connect with us

LABARAI

Buhari Ya Gargadi Shugabanin Jami’o’i A Kan Cin Zarafin Mata

Published

on


Shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci dukkan jami’o’in kasar da suyi maganin dukkanin matsalolin da ake fuskanta a harkokin gudanar da karatu, wadanda suka hada da cin hanci da rashawa da cin zarafin mata wadanda suka dade suna bata suna da mutuncin bangaren ilimi a kasar nan.
Shugaba Buhari ya yi wannan maganan ne a sakon daya aika ga bukin yaye dalibai karo na 29 dana 30 na jam’iar Jos, wanda ya gudana a filin wasa na Jeremiah T. Useni dake mazaunin jami’ar na dindindin a Naraguta a karshen mako.
Shugaba Buhari ya ce, gwamnati zata ladabtar da shugabanin jami’oin da suka ki dukan mataki a a kan korafe korafen cin zarafin mata da aka gabatar a makarantunsu.
Babban sakataren hukumar kula da jami’o’i (NUC) Farfesa Rasheed Abubakar ya wakilci shugaban kasar, inda ya ci gaba da cewa, dole jami’o’inmu su dabbaka akidar riko da gaskiya da mutumci da kuma aiki a bayyane ba tare boye boye bad a kluma tabbatar da doka da oda saboda su bayar da gudummawa wajen ci gaban kasar nan a bangaren tattalin arziki da siyasa da kuma bunkasar al’adunmu.
Jami’ar ta yaye dalibai 18,348 inda suka samu digiri masu matsayi daban daban kamar haka, dalibai 33 sun fita da digiri mai daraja ta daya (Distinction/First Class) yayin da dalibai 1,950 suka samu digiri mai daraja ta biyu (Second Class honours (Upper Dibision) sai dalibai 5,738 da suka samu digiri mai daraja ta (Second Class honours (Lower Dibision) dalibai 3,149 kuwa sun fita ne da digiri mai daraja ta uku (Third Class degree) yayin da dalibai 351sun fita da digiri mai matsayin (Pass) ba yabo ba fallasa.
Haka kuma dalibai 734 sun samu zama cikakkun Likitoci da masu hada magunguna, (Medicine and Pharmacy), yayin da dalibai 399 suka samu shaidar Difloma, dalibai 103 suka kammala karatu a bangaren (Post Graduate Diploma), yayin da dalibai 2,906 suka samu shaidar kammala karatu a bangaren (Post Graduate Programme (M.A and M.Sc), haka kuma dalibai 165 suka kammala karatu da matsayin Dakta (Ph.D).


Advertisement
Click to comment

labarai