Connect with us

LABARAI

Zamu Ci Gaba Da Tallafa Wa Marayun Garin Legas -Alhaji Ummaru

Published

on


Shugaban kungiyar bayar da tallafi ga marayu na jihar Legas, Alhaji Ummaru Lawan Atana Agege,wadda take karkashin jagoracin kungiyar Izalatu bidia waikamatus Suna ta jihar Legas, ya bayyana cewa, kugiyarsu zata ci gaba da tallafa wa marayu a kowanne Lokaci domin kyautata rayuwarsu.
Shugaban kungiyar ya yi wannan bayani ne a lokacin da dubban dubatan marayun jihar Legas suka sawo kayan sawa na wanna sallar idi da ziyarce ziyancen yan uwa da abokan arziki kuma suka zo masa yawon gaisuwar barka da sallah a offishin kungiyar dake a unguwan Woniwaya jokshon Alpah Lillah Agege, Alhaji Lawan ya ci gaba da nuna farin cikinsa ganin wadannan marayu sun zo ziyara da kuma barka da sallah adaidai wannan lokacin, sannan ya ci gaba da mika godiyarsa ga Allah madaukakin sarki da al’ummar musulmin Agege da jihar Legas baki daya a bisa gudunmawar da suke ba wanna kungiya a kowane lokaci domin ta ci gaba da gudanar da aiyukan alheri, ya kuma yi fatan ba zasu gajiya ba wajen tallafa wa aduk lokacin da bukatan haka ya taso.
A wajen karbar bakuncin marayun akwai dimbi jama’a da suka zo gane wa idonsu wannan aikin alheri da kungiyar ta gabatar da kuma yin fatan alheri game da wannan alamari
Alhaji Sani Sha’aibu Maigoro Agege na daya daga cikin iyayen wannan kungiyar kuma daya daga cikin wadanda suka assasata a Agege ya bayyana nasa farin cikin ne da godiya ga Allah da ya basu ikon ganin wannan lokaci na sallah da kuma ganin wannan shuka da suka yi ta alheri tana ta fitowa, ya kuma kara da cewa, shi da saura iyayen wannan kungiyar zasu ci gaba da taimaka wa kungiya don ta ci gaba da gudanar da aiyukanta na alheri, ya ce, ko a yanzu ma sunanan suna neman gidaje na sayarwa domin samarma marayun jihar Legas matsuguni.
Da yake nasa tsokacin a wajen karba bakuncin marayun, tsahon shugaban kungiyar Izalatul bidia waikamatus Sunna ta kasa Sheikh Buhari Yakubu Agege da maitamakin shugaban kwamitin gudanar da aiyyuka na Izalatul bidia waikamatus Sunna ta kasa bayan ya taya ‘yanuwa musulumi murnar kammala wannan watan azumi na bana da kuma nuna farin cikinsa game da wadannan kungiyoyi na tallafawa addinin musulucin suke gudanar da aiyyukan alheri kamar wadanan, ya kuma yi fatan zasu ci gaba irin wadannan aiyyukan alhairin.
Alhaji Sani Umar Sale Agege da sauran wadanda suka yi jawabi, sun jawabi sun yi wa kungiyar fatan alhairi a wannan namijiin kokari da suke yin a taimakon al’umma.


Advertisement
Click to comment

labarai