Connect with us

LABARAI

Za Mu Cika Burin Khalifa Na Ganin An Bude Jami’ar Kur’ani Da Ya Kafa A Kano –Alhaji Karami

Published

on


Daya daga cikin ya’yan khalifa sheik Isyaka Rabiu, Alhaji Rabiu Isyaka da ake yi wa lakabi da Alhaji karami ya ce, za su cigaba da ginawa da tabbatarda cika muradan mahaifinsu marigayi sheik Kalifa Isyaka Rabiu ta cigaba da abinda ya somo.
Alhaji karami wanda ya bayyana haka da yake zantawa da manema labarai bayan an kammala zaman makokin rasuwar khalifan a gidansa dake unguwar Goron dutse a jahar kano.
Ya ce za su cika burinda mahaifinsu sheik Khalifa Isyaka Rabiu ya rasu akai dan ganin an soma gudanarda karatu ajami’ar Kur’ani mai girma daya kafa a Gadon kaya.
Alhaji Karami Isyaka Rabiu wanda shine shugaban kamfanin jiragen Sama na IRS ya ce za su cigaba dayin aiki tukuru dan ganin an soma gudanarda Jami’ar ta Alkur’ani mai girma wanda tuni an cika ka’idoji da samun sahalewar hukuma .
Alhaji Rabiu Isyaka Rabiu ya ce Khalifa Uba ne da ya ba su tarbiya ta Al-kur’ani, zamantakewa da ta mu’amala. Kuma baya fifitasu a matsayinsu na ya’yansa dana waje saboda irin kulawa da yake baiwa jama’a.
Ya ce rashin na Khalifa rashine daya shafi kowa ba Kasarnan kadai ba harma da kasashen Afurka dama Duniya baki daya.
Alhaji Karami Isyaka Rabiu yayi godiya mutuka ga dukkan ilahirin wadanda sukazo daga ciki da wajen kasarnan danyi musu ta’aziyya na rashin Khalifa Isyaka Rabiu wanda ubane,jagorane daya sadaukarda ransa tun daga kuruciya har komawarsa ga ubangiji wajen hidima ga littafin Allah da ba dare ba rana kuma suma za su cigaba da tsayuwa akan gwadabenda yake har zuwa karshen rayuwarsu ta raya wannan dashe da Khalifa Sheik Isyaka Rabiu yayi.
Shi ma a nasa bangaren Gado da masun Kano, Alhaji Ahmad Maiturare ya bayyana Khalifa Isyaka Rabiu da cewa bangone ga yan kasuwa domin shine yake basu kaya yayi maka ragi sosai da za su sami riba akai,idan ma bakada jarin ya baka.
Mai turare ya ce yana alfahari da tarayyarsa da marigayi Khalifa Isyaka Rabiu wanda ya daukeshi tamkar dansa kodayaushe yana sa shi a al’amuransa


Advertisement
Click to comment

labarai