Connect with us

LABARAI

Sojojin Nijeriya Sun Kashe Barayin Shanu 20 A Zamfara

Published

on


Rundunar Soji ta 1 da ke Kaduna, ta fada a ranar Asabar cewa, ta kashe ‘yan ta’adda 20 ta kuma kama wasu guda uku a kauyen Jambrini, da ke karamar hukumar Maru ta Jihar Zamfara.
Mataimakin daraktan yada labarai na rundunar, Kanar Muhammad Dole, ne ya fadi hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a Kaduna.
Kakakin ya ce, rundunar Sojin cikin farmakin da take kaiwa mai lakabin, ‘Operation IDON RAINI Corridor II,’ ta farmaki wata maboya ce ta ‘yan ta’addan a sassan kauyan na Jambrini, da jijjifin safiyar ranar 23 ga watan Yuni.
A cewarsa, a lokacin farmakin, sun lalata maboyan ‘yan ta’addan masu yawa, sun kuma kashe 20 daga cikinsu.
“Mun kuma kama ‘yan ta’adda uku, sa’ilin da da yawa daga cikinsu suka tsere da raunukan harbin bindiga,” in ji shi.
Ya lissafta abubuwan da suka kwato daga hannun ‘yan ta’addan da suka hada da bindigar AK47 guda 4, karamar bindigar F99 guda daya, wata wayar hannu samfurin, PTT HH Motorola, guda daya, albarusai 111, kwanson harsasan bindigar AK47 guda biyar, bindigogi kirar gida guda biyu, wayoyin hannu guda uku, da kuma bankin cajin waya guda daya.
Dole ya ce, rundunar ta lashi takobin kakkabe ayyukan ‘yan ta’addan daga yankunan bakidayansu.
Ya ce, sun sami nasarar hakan ne ta hanyar bayanan da wasu mutanan kirki da ke yankunan suka kai ma su.
“Muna rokon al’ummu da su rika sanar da mu da sauran dukkanin jami’an tsaron da muke aiki tare da su, labarai tabbatattu,” in ji Kanar Dole.


Advertisement
Click to comment

labarai