Connect with us

LABARAI

Hadin Kai Ne Sirrin Ci Gaban Al’umma—Inji Sarkin Yamma Katsina

Published

on


An bayyana cewa, tabbatar da hadin kai tsakanin al’umma shi ne babban sirrin dake kawo ci gaban dukkan bangarorin rayuwar al’umma, musamman a wannan zamanin dam eke ciki. Maigirma sarkin yamman Katsina Hakimin Faskari Alhaji Tukur Usman Sa’idu Faskari ne ya yi wannan kira ga al’ummar garin Yankara dake karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina, ya bukaci su hada kansu domin ci gaba a yankin masarautar Faskari da jihar Katsina baki daya.
Basaraken ya yi wannan kiran ne lokacin da tawagar Barayan Faskari Alhaji Shehu Usuman Sallau da Sarkin Fadar ‘Yankara suka kai masa gaisuwar bangirma da barka da sallah a fadarsa dake garin Faskari a ranar Alhamis 21 ga watan Yuni 2018.
Tun farko mai magana da yawun Barayan Faskari, Malam Muhammad Lawal Galadima ya shaida wa Sarkin Yamman Katsina cewa, makasudin zuwan su shi ne domin kawo gaisuwar bangirma da kuma yi masa barka da sallah. Wannan na faruwa ne bayan Barayan ya dawo daga jinyar da ya kwashe watani biyar yana yi sakamakon hadarin motar da ya samu sanda zai zo gida daga Kaduna. Kuma abin yasa kaga dinbin mutane haka shi ne irin nuna kaunar da yake yi wa garin na ‘Yankara da kuma taimakon al’umma, hakan yasa kusan dukkan bangarorin jama’ar garin sun samu wakilci wajen rufa wa Barayan baya don kawo wannan ziyarar.
A nasa jawabin, Barayan na Faskari Alhaji Shehu Usman Sallau ya gode wa Sarkin sosai daya “Bamu dama muka kawo masa ziyara duk da dinbin hidindimun jama’a dake gabansa.
Sarkin Yamman ya nuna jin dadinsa yanda yaga Barayan ya samu sauki sosai, daga cikin wadanda suka rufa masa baya akwai kungiyoyi daban daban na garin ‘Yankara kamar kungiyar ‘yan achaba dana NURTW da kuma kungiyoyin magina da makera da ‘yan kasuwa da ‘yandirama da kuma Limamai da ‘yan sintiri da sauransu, haka kuma tawagar ta samu halartar wani babban manomin nan kuma dan kasuwa mai suna Alhaji Hamisu Tanko, inda ya mika godiyarsa ga matasa da sauran mutanen garin ‘Yankara a bisa soyayyar da suke nunawa Barayan, ya kuma gode wa Barayan ya kuma bukaci ya ci gaba da hidimar da yake yi ga al’umma, musamman abin daya shafi tallafi wajen karatu da sana’o’i ga dimbin matasa, ya kuma bukaci matasa su rungumi zama lafiya da kaucewa tashin hankali musamman a lokacin harkar siyasa dake tafe.


Advertisement
Click to comment

labarai