Connect with us

LABARAI

Gwamna Ganduje Ya Bayyana Alhinin Rasuwar Kansila Da Shugabannin Jam’iyya Biyu A Kan Hanyarsu Ta Zuwa Abuja

Published

on


Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje Ya bayyana mataukar girgiza bisa rasuwar Kansilan Mazabar Diso daga Karamar Hukumar Gwale tare da wasu mutane biyu wanda wani mummunan hadari ya rutsa dasu akan hanyar su ta zuwa Abuja domin halartar taron Jam’iyyar APC na Kasa.
Wadanda hadarin ya rutsa dasu sun hada da Abdulwahab Inusa Kansilar mazabar Diso, Alhaji Abdullah Lawan Dattijon Jam’iyyar APC da kuma Abubakar Farouk Ibrahim Sakataren Jam’iyyar APC na Mazabar Diso. Da yake mika sakon ta’aziyyar wanda Kwamishinan Yada labarai, Matasa da wasanni na Jihar Kano Malam Muhammad Garba ya rabawa Manema Labarai, Gwamna Ganduje ya yi addu’ar Allah ya gafarta kurakuransu, haka kuma ya bayyana matanen da cewa ‘yan kishin kasa ne masu cikakkiyar biya ga Jam’iyyar APC.
Gwamna Ganduje ya bayyana mamatan da cewar halattattun ‘yan Jam’iyya ne wadanda ke bayar da gudunmawa kwarai da gaske ga ci gaban Jam’iyyar APC , zaman Lafiya da ci gaban Jam’iyyar APC wanda za’a jima ana tunawa da gudunmawar wadannan mutane. Saboda haka sai Gwamna Ganduje ya yi addu’ar fatan Allah ya gafarta masu ya baiwa iyalansu juriyar wannan babban rashi


Advertisement
Click to comment

labarai