Connect with us

LABARAI

Gidauniyar Dan Lawan Ayuba Ta Yi Taron Sada Zumunci

Published

on


Anyi kira ga Gwamnati ta kara kokari wajen samarda aikinyi ga matasa dan kawarda daba da shaye-shaye dan samarda ingantaciyar al’umma. Kwamandan humar tsaro na farin kaya Sarki Aliyu Daneji ya bayyana haka wajen taron shekara na sada zumunci da Gidauniyar Dan lawan Ayuba gudanar a dakin wasa na Sani Abacha.
Ya ce shi zumunci umurnin Allah ne ayi kokari wajen sadashi tareda neman ilimi dan magance irin abinda ke faruwa a rayuwa ayu na tsintar kai ga tabarbarewar tarbiyya.
Daneji ya ce ya ce tarone na zumunci dake tara yan’uwa da ake sanin juna a irin wannan haduwa ya kuma yabawa masu shiya taron bisa jajircewa da kokarinsu.
Tun a a jawabinsa farko ma’ajin Gidauniyar ta Dan Lawan Ayuba ya bayyana cewa an kafa gidauniyarne dan habaka zumunci da suka soma basufi su 20 ba,har suka fadada abin zuwa yanzu da ake karo na uku.
Malam Abdurra’uf Umar Adam ya ce shekaru Biyar kenan da kafa Gidauniya amma wannan ne taronsu na uku na shekara dake hada su. Sun kuma habaka taronne ta ziyarce-ziyarce da shawarwari da tuntuba ta kafafen sada zumunci na zamani. Duk taro dangi samada mutane 1000 na taruwa tunda suka soma. Sun kuma hada auratayya da taimakekeniya a tsakani ta bangarori daban-daban.
Abdulra’uf yayi kira ga al’umma su daure wajen sada zumunci ta irin wannan taro dan hada fuskokin yan’uwa dan sanin juna. Ya zayyano tsare-tsaren ayyukan Gidauniyar da kuma abubuwanda sukasa a gaba dan habakata tareda kiraga Dangin su cigaba da bada gudummuwa musammam na tallafi ga kungiyar dan cigabanta.
A taron an karrama zannan kano Alhaji Aminu Sadik da Kwamanda Sarki Daneji da Hajiya Bilkisu da Alhaji Bello Goranyo da sauran dangi na iyalan gidauniyar Dan Lawan da suka fito daga sassan kasar nan daban-daban.


Advertisement
Click to comment

labarai