Connect with us

LABARAI

Gidan Yari Wurin Gyara Tarbiya Ne Ba Wurin Musgunawa Kowa Ba -Kwanturola Magaji

Published

on


An Bayyana gidajen Yari da cewa gidaje ne na gyaran tarbiyya ba wuraren musgunawa wani bane, wannan bayani ya fito daga bakin Kwanturolan gidajen yarin Jihar Kano Alhaji Magaji Abdullahi alokacin da yake zantawa da Jaridar Leadershipa a yau. Magaji Abdullahi ya bayyana cewa akwai rashin fahimtar da wasu ke yiwa harkokin gidajen yari, musamman yadda wasu kan fassara Kalmar Gidan Yari ko Jarun ko gidan kaso, wanda duk wadannan sunaye ana kallonsu a matsayin wurin kaskanci.

Kwanturolan yace gidan yari gida ne mai dadadden tarihi domin tun fil-azal akwai gidajen yari, wuri ne da ake ajiye masu laifuka domin girbar hukunci abinda suka shuka, kuma alhamdulillahi mu anan muna daukar duk wanda ya shigo wannan gida a matsayi danmu, muna yin duk mai yiwuwa wajen kokarin gyara tarbiyarsa ta yadda idan ya fita zai zama ingantaccen mutun mai cikakkiyar daraja da kuma amfani ga al’umma.

Magaji Abdullahi yace babban abinda yafi damun mu shi ne yadda ake kafawa wadanda suka fita daga gidan yarin kahon zuka tare da nuna tsangwama garesu, hakan alokuta da dama kan sa su sake aikata wasu laifukan da za’a sake dawo dasu cikin wannan gida, a ganinsu gara ma zama a irin wannan gida da irin tsangwamar da ake nuna masu bayan fitarsu daga sarka.

Da yake karin haske kan irin ci gaban da gidajen yari suka samu a wannan lokaci, Kwanturolan na Jihar Kano ya bayyana cewa wannan nasara ta samu sakamakon samun jajirtaccen shugaban Hukumar Gidajen yari na kasa Alhaji Jafaru Ahmad wanda yake aiki ba dare ba rana wajen tabbatar da ganin an samu kyautatuwa tsari a gidajen yarin kasar nan. Saboda haka mu anan jihar Kano muna da gidajen yari guda goma, amma zuwa wannan lokaci ina tabbatar maka da cewa idan ka shiga wani gidan yarin musamman na Kurmawa sai ka bata domin anyi sabbin gine-gine harda benaye aciki, duk wannan ginin Kasar an kawar dasu tare da maye gurbinsa da gini irin na zamani.
Ya ci gaba cewa haka batun tsarin ciyarwa duk wannan shugaba namu ya kawo ci gaba ba kamar yadda suke a shekarun baya ba, ga kuma tsarin koyar da sana’u da ilimi tun daga matakin ilimin manya har zuwa digiri da digirgir ana samu a gidajen yari. Don haka muke jadadda godiyar mu bisa Jagorancin Alhaji Jafaru Ahmad tare da tabbatar masa da ci gaba da bashi dukkan hadin kan da yake bukata wajen cin nasarar abibda da aka sa gaba.


Advertisement
Click to comment

labarai