Connect with us

LABARAI

An Kama Mutun Uku Da Ake Zargi Da Kashe Danmajalisa A Taraba

Published

on


Rundunar ‘yan sandan jihar Taraba ta nuna wasu mutum uku a Jalingo da ake zarginsu da laifin yin garkuwa tare da kashe danmajalisar wakilai mai walkilta mazabar Takum, Mista Hosea Ibi.
Da yake yi wa manema labarai jawabi kwamishinan ‘yan sandar jihar, Dabid Akenrimi,ya bayyana sunan wadanda ake zargin, Muwagha Iorsbagha da Aondouga Hundi da James Gun.
Ya ce, kuma dukkansu mazauana kauyen Chekwaza da ke karamar hukumar Katsina-Ala, a jihar Binuwai.
Akenrimi ya bayyana cewa, wadanda ake zargin tare sa shugabansu, Andofa,sun yi garkuwa da Mista Ibi a watan Disambar bara daga gidansa da ke cikin garin Takum.
Kwamishinan ya ce wadanda ake zargin sun tabbatar da laifinsu cewa sun kama danmajalisar a gidansa suka kai shiumwajen shugabansu, daga karshe suka kashe shi.
Lokacin da wadanda ake zargin ke amsa tambayoyin manema labarai, sun ce wani babban dansiyasa ne ya dauki hayarsu domin su dauko Mista Ibi su yi garkuwa das hi sannan kuma su kashe shi.
Haka kuma sun ce dan siyasar ya yi alkawarin zai saya musu mota, amma bai cika musu alkawari ba.
Kwamishinan ya ci kara da cewa, sun kama masu laifin ne bayan sun yi masayar wuta da ‘yan sanda a karamar hukumar Bali.
In dai za a iya tunawa masu garkuwar sun karbi kudin fansa Naira miliyan 25 a hannun iyalan marigayi danmajalisar kafin su kashe shi.


Advertisement
Click to comment

labarai