Connect with us

LABARAI

An Damke Sanata Abaribe Ne Da Tuhumar Safarar Makamai, Inji Lauya

Published

on


Wani babban Lauya mai mukamin SAN, Chukwuma-Machukwu Ume, ya ce, jami’an tsaro na DSS sun kama ne tare da tsare, Sanata Enyinnaya Abaribe, a ranar Juma’a, bisa tuhumarsa da suke yi da mallakan bindigogi ba bisa ka’ida ba da manufar taimaka wa kungiyar nan ta ‘yan asalin Biyafara da aka soke ta, ‘Indigenous Peoples of Biafra.’
Lauyan na Abaribe, wanda ya tabbatar wa manema labarai da hakan a Abuja ranar Asabar, ya ce, wannan zargin shi ne a cikin takardar warantin binciken da jami’an tsaron na DSS suka gabatar a gidan dan Majalisar da ke Apo, ranar 22 ga watan Yuni 2018, sa’ilin da suka isa gidan.
Lauyan ya ce, Jami’an tsaron sun kwashe sama da awanni shida suna bincike a gidan ranar ta Juma’a.
Lauyan ya ce, “Cikin dukkanin ababe 27 da suka karbe a gidan suka kuma ta fi da su, ba daya daga cikin abin da suke nema din, kamar yadda suka ce wai sun zo neman bindigogi ne da albarusai gami da jakunkunan kudin da aka taskace domin taimaka wa ‘yan tawayen na biyafara.
“Abin takaicin, biyu daga cikin abubuwa 27 da suka amshe a gidan, wayoyin sadarwa na hannu ne mallakin wasu Amerikawa biyu da suke gidan. Daya kuma daga cikin kwamfutocin hannun da suka ta fi da su, na wani dalibi ne wanda a yanzun haka yake yin jarabawarsa da su.
“Duk rokon da dalibin ya yi na a bar shi ya kwafi tambayoyin jarabawar na shi, sun ki yarda.”
Lauyan ya ce, akwai damuwa kan yadda lamurran ke ta faruwa, musamman ganin cewa, a watan Oktoba 2017 ne, ya kamata Nnamdi Kanu ya sake komawa Kotu, amma sai aka kai ma shi farmaki a gidansa a watan Satumba.
Abaribe, wanda shi ne ya tsaya wa Nnamdi Kanu din, zai bayyana ne a gaban Kotu a ranar 26 ga watan Yuni 2018


Advertisement
Click to comment

labarai