Connect with us

LABARAI

Manufar Kungiyarmu Shi Ne Karewa Da Alkinta Muhalli –Dr. Mai’Abba

Published

on


Wata kungiya mai rajin inganta albarkatun kasa da hana sare daji mai suna (Natural Resources Conserbation Foundation) a Jihar Bauchi ta shawarci gwamnati da ta dauki matakin gaggawa game da hana sare bishiyoyi da daji barkate saboda hana kwararowar Hamada da kuma kare halittu masu yawa da ke rayuwa a cikin daji da muhallin da ke kasar nan.

Shugaban kungiyar Dokta Ahmed Mai Abba shi ne ya yi wannan kira cikin taron manema labarai da suka kira jiya a Bauchi inda ya bayyana cewa sun kafa wannan asusu ne ko kungiya bayan zaman tattaunawa da wasu manyan mutane a Jihar Bauchi wadanda suka damu da matsalolin da muhalli ke ciki a wannan lokaci. Don haka suka nemi rijista da hukumar yiwa kungiyoyi rijista ta kasa (CAC)  kuma suka samu takardar shaida cikin watan Aprilu na wannan shekara inda aka mikawa shugabannin kungiyar daga nan kuma suka zauna a watan mayu suka kaddamar da kungiyar suka ci gaba da tattaunawa. Don haka ya ce muhimmin aiki da wannan kungiya ta sa a gaba shi ne kare muhalli da albarkatun cikin sa da kuma kare gandun daji da albarkatun kasa da halittun da Allah ya samar don amfani mutane a duniya.

Dokta Mai Abba ya kara da cewa kudirin wannan kungiya shi ne ta kare kasa da abin da ke cikin ta da kuma ruwa da iska da bishiyoyi da dabbobi da kwari don samun ingancin amfanin su ga dan adam, amma kuma son zuciyar wasu mutane ya sa ana lalata su ko ana amfani da su ta hanyar da bata dace ba yadda daga bisani sakamakon ya ke kasancewa na wahalar da duniya da mutanen cikin ta musamman a wannan kasa da wasu kasashen Afirka. Yadda ambaliyar ruwa da tsananin iska ko shan gurbatacciyar iska ke wahal da mutane.

Ya kara da cewa a wannan lokaci dan adam na gurbata ruwa da iska da masa’antu da ake ginawa wadanda suke gurbata muhalli ta hanyar zubar da dagwalo da gurbata iskar shaka, a madadin a rika kafa masana’antun a nesa da muhallin da mutane ke zama. Irin wannan matsala tana cusa cututtuka a cikin iska da ruwan sha yadda mutane ke kamuwa da cututtukan da a wassu lokuta ke zama sanadin rayuwar mutane. Bayan haka kuma wasu mutane na gini a kan muhalli suna haifar da ambaliyar ruwa da rushewar gine gine a sakamakon rufe magudanun ruwa da ake yi a wannan lokaci.

Dokta Ahmed Mai Abba ya kara da cewa wannan kungiya mai zaman kanta na da shugabanni guda biyar wadanda sun rike mukamai wasu kuma sun taka rawar gani a fannin ci gaban rayuwar jama’a. Don haka manyan manufofin da suka sa a gaba sune jan hankalin jama’a da gwamnati wajen tabbatar da ana kwashe shara a kan lokaci da shuka bishiyoyi da kuma yashe magudanun ruwa da yaki da kona daji da sauran dangogin matsalolin da ke jawo illa wa muhalli. Wannan kungiya ta kudiri aniyar hada kai da gwamnati kamar su hukumar muhalli ta BASEPA da ma’aikatar kasa da ta muhalli da kungiyoyi don wayar da kan jama’a game da yadda za a alkinta muhalli mutane su fita daga mawuyacin halin da suke ciki a sakamakon lalata muhalli da wasu mutane ke yi.

Don haka ya bukaci ‘yan jarida su taimaka don wayar da kan jama’a saboda ba wani aiki da zai ci gaba sai an wayar da kan mutane, kuma yin hakan shi ne zai taimaka wajen inganta yayuwar yara masu zuwa don su rayu a muhallin da za su yi farin ciki da shi, don haka suke neman tallafin ‘yan jaridu na takarda da radiyo da talabijin da kungiyoyi masu zaman kan su NGO don samun nasarar wannan aikin a Jihar Bauchi da sauran sassan kasar nan.

 


Advertisement
Click to comment

labarai