Connect with us

LABARAI

Hukumar Gidan Yari Ta Bukaci Guraben Karatu Ga Daurarru A Jigawa

Published

on


Hukumar Kula Da Gidan Yari (NPS), reshen jihar Jigawa, ta bukaci Jami’ar Karatu daga gida wato ‘National Open Unibersity of Nigeria (NOUN)’ da ta samar da izinin karatu a jami’ar wa daurarrun da suke gidan yari a Jigawa.

Kwantilona na hukumar a jihar Jigawa, Alhaji Auwalu Diso shine ya shaida bukatar a lokacin da ya halarci taron rantsar da sabbin daliban jami’ar karatu daga gida na rukunin 2017/2018 wanda ya gudana a jiya Asabar a garin Dutse.

Diso, wanda ya samu wakilcin Sifiritandan hukumar, Mr Saidu Kibiya, ya ce kamar kowani dan gidan yari a Nijeriya, daurarun da suke Jigawa za su iya karatu a jami’ar karatu daga gida wato NOUN.

Ya bayyana cewar tsarin ya taimaka wa daurarun gidan yari da dama wajen samun nasarar yin karatu a matakan digiri, mastas har ma da digirin digirgir a fannoni daban-daban na ilimi.

Ya ce, “Ina mai farin cikin sanar da ku cewar wanna tsarin ya taimaka sosai wajen canza dabi’un ‘yan gidan yari da dama. A takaice dai, ‘yan gidan yari da dama sun sauya halayensu da kuma gyara kura-kuran da suka tafka har suka samu kansu a daure,”

“A bisa haka, muna sake neman NOUN da ta yi la’akari da bukatunmu na sake baiwa daurarru damar kartu a jami’ar” In ji shi.

A gefe guda kuwa, jami’ar karatu daga gidan reshen Dutse ta rantsar da daliban 210 a rukunin 2017/2018 a wannan karon.

Mai rikon mukamin Daraktan cibiyar ilimn, Malam Abdullahi Ya’u, ya shaida cewar ya shaida cewar an samu ci gaba sosai idan aka yi la’akari da zangon karatu na 2016/2017.

Ya yi amfani da damar wajen yin kira ga jama’an da suke jihar Jigawa musamman ma’aikatan gwamnati da sauran ma’aikata da su yi amfani da wanna damar wajen samun damar zurfafa karatunsu a wannan jami’ar ta karatu daga gida.

Ya bayyana cewar a jami’ar NOUN ne kadai mutum zai samu nasarar yin karatu cikin kwanciyar hankali.

Ya bayyana cewar jami’ar ta NOUN yanzu haka an da cibiyoyin koyar da karatu 78 a fadin kasar Nijeriya.

A gefe guda kuma ya bukaci sabbin daliban da su kasance masu bin dokoki da ka’idojin jami’ar domin samun nasarar yin karatu mai nagarta.

 


Advertisement
Click to comment

labarai