Connect with us

TATTAUNAWA

Har Yanzu Arzikin Shekarau Buhari Ya Ke Ci, Cewar Yarima

Published

on


ALHAJI YAKUBU YARIMA fitacce kuma tsayayyen dan siyasa jigo a jam’iyyar PDP sannan kashin bayan tafiyar siyasa a gidan Malam Ibrahim Shekarau, inda Yarima shi ne mai bai wa tsohon gwamnan jihar ta Kano shawara kan harkokin siyasa. Wakiliyar LEADERSHIP A YAU LAHADI, BILKISU YUSUF ALI, ta tattaunawa da Yarima a birnin Kano. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Me Gidan Sardauna Shekarau ke ciki game da zaben 2019?

Alhamdilillah, kamar yadda kowa ya sani ne mu yanzu a cikin PDP abinda ya faru ya riga ya faru, babu irin abubuwa da ba a yi ba domin a dakushe tagomashi da daukaka da farin jini da haske na jam’iyyar, amma wannan ba ta hana a lokacin da ake tsaka da wannan tsangwama saboda an jingina karya da sharri da abin da yake samun kasar nan na rashin tsaro aka jinginawa PDP ko a lokacin wannan ba ta hana mu mu yi tallan tsohon tsugaban kasa ba Dr Gudluck Jonathan da jam’iyyar PDP a jahar Kano saboda mutanen Kano sun san wa ye malam Ibrahim Shekarau sun san me ya yi musu har tsahon shekara takwas.Wannan ya sa daga sassa daban-daban ake ganin dacewar Malam Ibrahim Shekarau ya fito ya nemi takarar shugabancin kasar nan kamar yadda ya yi ashekara ta 2011 ya tsaya takara kuma an jefa masa kuri’a kuma ya ci primary election har ya kai ga secondary election. A yanzu ma abin da ‘yan Najeriya ke fata Kenan suke kira ya yarda ya amince ya fito ya yi takara a jam’iyyar Najeriya jam’iyyar ‘yan Najeriya jam’iyyar kowa da kowa jam’iyyar PDP. Kuma Mai girma Sardaunan Kano ya yarda ya amince zai yi takarar neman shugabancin kasar nan a Inuwar jam’iyyar PDP a shekarar 2019.

 

Ta ya ka ke ganin zai iya samun tikitin takara a PDP?

Ai takarar maigirma sardaunan Kano ba ta a mutu ko a yi rai ce ba takara ce da ‘yan Najeriya suka nema. Mu kuma a wajenmu a zawarawan nan na jam’iyyar PDP dukkanninsu masu kyau ne ba mu da na yarwa amma in son samu ne mun fi son a ce maigirma sardaunan Kano shi ne aka tsayar saboda duba da yadda ya haifar da ci gaba a jihar Kano da ma kasa gaba daya lokacin a yake minister.Wannan ya sa muke ganin idan ya zamo dan takara a jami’iyyar PDP zai fi saurin kayar da wannan shugaban kasar da ke ci yanzu. Don haka muna so, muna fata ‘yan Najeriya da ‘yan jam’iyyarmu masu albarka su ba shi dama don shi ya taba tsayawa takarar ya kai har babban zabe. Muna da tabbacin in aka ba shi dama zai kada shugaban kasa na yanzu.

Ko ma’aikata kadai ka dauke su a lokacin gwamnatin maigirma Sardauna ka san sun isa hujjar ya zama shugaban kasa. A lokacinsa ya mayar doka ya yi tsari duk ma’aikaci in watan azimi ya kama za a ba shi kudin gero. Idan sallah babba ta zo a ba shi kudin rago duk don mu kyautata wa al’umma. Ai yanzu ga azimin ya zo ma’aikata sun fi kowa shiga matsala kullum sai ma’aikatan gwamnati sun zo gidana suna neman taimako. Ba kuma ni kadai ba, ni da ma ba ni da gwamnati. Wannan taimakon da Malam Ibrahim Shekarau ya bayar bai isa ya hana kome ba amma mutum zai ji dadi wannan kyautatawa ce. Amma a wanann gwamnatin, albashinma ma’aikatan ma ba su da tabbas dinsa wannan watan in ka ga an debi kaza wani watan sai a rage kaza ma’aikata ba su ma da tabbacin albashinsu.

 

A na cewa tsayar da dan takara magana ce ta kudi, saboda deliget. Ku na da kudi ne?

Ba Magana ce ta kudi ba, jam’iyyar PDP jam’iyya ce da ake yin cikakkiyar damukuradiya in da ba kudi ke sa wa a ci zabe ba don kudi ke sa wa da maigirma sardauna bai ci zaben shekara ta 2003 ba, har ya zama gwamnan Kano kuma da bai zama gwamna a shekara ta 2007 ba. Allah da y a ba shi a wancan lokacin shi muke roka ya ba shi yanzu, ai a wancan lokacin ma akwai deligate din. Mun tabbatar daga nagartattun ayyukan da Sardaunaya yi wanda za mu zo mu bayyanawa ‘yan Najeriya da ‘yan jam’iyyar PDP za su gamsu ba deligate ba ko wa ye zai yi zabe na tabbatar in sha Allahu in zai yi zabe zai zabi maigirma sardaunan kano, ba sai ya ba da komai ba. Domin malam bai tara kudin da zai bayar a zabe shi ba mu damokuradiya muka sani me ka yi wa al’umma me kuma muke da burin za mu yi nan gaba.

 

Da me za ka auna Malam Ibrahim Shekarau ya dara da sauran ’yan takara?

Tunda siyasa ake yi akwai abubuwa da yawa na farko Dr Malam Ibrahim Shekarau ya yi gwamntatin Kano ya yi abubuwa da dama mu dau abubuwa guda uku muhimmai mu dau bangaren ilimi a lokacin da yana gwamnan Kano sai da ya gina makaranta , ginawa ba gyara ba sababbi guda dari biyar da saba’in da wani abu. Ya samar da matatar ruwa da duk Afrika babu kamarta ya yi ta a Tamburawa a kudin da bai kai kaso goma a yanzu da wasu suka yi ba.Misali jahar Lagas ta yi. A bangaren harkar lafiya nan ma maigirma malam Ibrahim shekarau a lokacin mulkinmu ne muka far aba wa duk wata mace mai ciki da haihuwabmagani da haihuwa kyauta domin mace it ace ginshikin al’umma. Maigirma malam Ibrahim shekarau yana ba wa mata muhimmancci sosai hatta karatun mata a lokacinsa kyauta ne. A lokacin Malam Shekarau magani kyauta ne a asibitoci. Kafin mu gama mulki sai da malam ya gina manyan asibitocin da duk Najeriya babu irinsu asibitin Giginyu da Zoo Road kafin mu sauka daga gwamnati Allah bai sa mun karasa su ba. Amma jin dadin aikin ya sa a aloacin da shugaban kkasa ya zo saboda babu wani aiki da ya fi wannan project din akan ya bude wannan aikin ya zo jihar Kano.Kuma ba aikinsu ba ne aikin maigirma Sardauna ne.Ayyukanmu duk da ingancin wadanda suka fito takara a PDP babu wanda ya yi aikin da ya sha gaban namu. Da irin wadannan abubuwan nake ganin idan mun bijirowa da ‘yan Najeriya idan mun bijiro musu da maganar takara za su yarda da Malam Ibrahim Shekarau.Don shugaban kasa mai ci na yanzu bas hi da irin wannan project din da zai iya nunawa ‘yan Najeriya wanda za su gamsu.

 

PDP a yanzu a na ganin tagomashinta ya yi kasa. Ya ka ke ganin za a cimma nasara a haka?

Sai ki je ki tambayi ‘yan Najeriya mun yi taro a Katsina mahaifar Shugaban kasa ‘yan Najeriya sun gay a muka yi wannan taron sannan mun yi taron jam’iyyar PDP a Jigawa shi ma ‘yan Najeriya sun ga yadda abin ya kasance anan jihar Kano mun yi taron jam’iyyar PDP mutane ne shaida. Al’ummar kasar nan sun yarda duk abin da malam Shekarau yake kai suna karbarsa don sun san mai kaunarsu ne sun yarda da irin kyawawan ayyukansa da kudirinsa na alheri kan su.

 

PDP din dai ka na ganin jama’a za su iya zabar ta?

Kwarai kuwa ai da ma karya aka yi da addini aka yi karya da tashin hankali da yaudara da rashin zaman lafiya da boko haram .Yanzu ‘yan Najeriya za su yarda da mu boko haram din nan yanzu daina ta aka yi? Har yanzu ana yi ga ma kari rigimar makiyaya da ake yi. Dauki jahar Zamfara kadai da abin da yake faruwa da jahar Kaduna abin takaici ne da Allah wadai da kaico. Abin kunya da tir gwanda wancan shugaban kasar ma ba soja ba ne amma wannan soja ne ga ma shi ne ma kwamanda in cif na sojojin Najeriya a zahirance ba wai a kundin tsari na kasa ba. Amma wancan dakta ne na ilimi amma wannan janar ne a soja amma yau an wayi gari ta’addanci ya fi wanda aka yi a baya in ka dauki adadin mutanen da aka kashe a Zamfara in ka hada su da mutanen da ake kashewa a Binuwe da Nasarawa da Birnin gwari da wadanda ake sacewa ya fi ta’addancin da ake yi a Maiduguri. Shi kuma wannan mai za ka kira shi jam’iyyar APC Kenan tunda baya an ce jam’iyyar PDP ce. In a baya jam’iyyar PDP an zarge ta saboda shugabanta to kuma me za a fadawa ‘yan Najeriya a yau ga dai gwamnatin APC tana kai kuma ta kasa magancewa da ai cewa ma ake duk dan PDP kafiri ne ni na kai lokacin da za mu yi sahun sallah sai ka ga mutane na ja da baya. yau wannan al’ummar su ne suka zo suma tuba a wajenmu yaudararsu aka yi da karya da addini yanzu sun gane mutanen nan makaryata ne ba za su iya ba.Daga abin da yake faruwa ai Jonathan shi ya fara yunkurin yadda zai dakile boko haram amma a lokacin da aka fara daukar matakai sai aka ce ai gashi nan zai fara kashe mutane saboda ba musulmi ba ne.

Da ya ke Allah ba ya bacci yau an wayi gari jahar Zamfara kadai ta gagari ministan tsaro tsohon soja ne janar haka shugaban kasa shi ma janar ne a asoja ya kasa magance rigimar Zamfara da birnin gwari ga ta Binuwai.Ina tsaron yake ? muna godewa jami’an tsaro godiya. Muna addu’a kan jami’an tsaronmu Allah ya ba su karfin gwiwa don murkushe ta’addanci don in ka bar wa wannan gwamnatin ba abin da za ta iya. Mun ji ma an ce ya ce yana son nan da sati biyu tsaro da zaman lafiya ya dawo Zamfara amma abin kunya washgari mutanen nan suka zo suka baza kauyuka wajen guda bakwai suka dauke dukiyoyinsu wannan a bayyane ake yin su. Ina tsaron ya ke? har yanzu akwai ta’addanci kuma ba kwanciyar hankalin.Yanzu dai ‘yan Najeriya sun gane ba jam’iyyar PDP ce ba.

 

An ce PDP a Kano na zawarcin tsohon gwamna Kwankwaso. Shin ku na son kara karfi ne?

Wannan ai siyasa ce ai duk wanda ke APC har ya zama wani ko shugaba albarkacin malam Ibrahim Shaikarau ya ci hatta shugaban kasa albarkacin malam Shekarau ne tarihi ba zai taba mantawa da shi ba tarihi ba zai kankare Shekarau ba babu wata kalma sadara daya a tsarin mulkin jam’iyyar APC da ba malam Shekarau ne ya rubuta ba. Idan kuma akwai a jarida na fada kafar yada labarai a fito a kalubalance ni duk abinda aka rubuta na tsarin mulki da dokoki na jam’iyyar Malam shekarau ya rubuta shi. Saboda haka maganar jam’iyyar APC su suka kafata kuma sun kafata ne da kyakkyawar niyya amma aka samu wasu marassa kishi suka kashe ta suka lallata ta suka lallata manufofinta da su Malam Ibrahim Shekarau suka tsara a kai. A yau duk jiga-jigan da suka kafa jam’iyyar APC ba sa nan. Ina Tom Ikoma yake ina Garba Gadi ina shi maigirma Dr malam Ibrahim Shekarau ina Buba Galadima wadanda sune yan zalakoko ‘yan ihu su ne ‘yan kaza Buhari komai Buhari ina irin su Naja ina irin su Sule Yahya Hamma yau fa duk wadannan mutanen da ma wasu jiga-jigan Buharin basa nan ba sa tare da Buharin. Shi kansa Buharin arzikin malam Shekarau din ne yake ci na fada na kara fada Buhari arzikin malam Shekarau yake ci domin Ibrahim Shekarau yana cikin kashin bayan gina APC.

Don haka in an ce irin su Sen Rabi’u Musa Kwankwaso da irin su Gwamna Tambuwal jam’iyyar PDP a baya ta bata musu rai suka ga maimakon su zauna suka ga gara su fita. Haka shi ma Malam Ibrahim Shekarau shi ma ya fita daga APC wanda ba Eng Rabi’u Kwankwaso ne ya sa Shekarau ya bar APC ba kin gaskiya da rashin adalcin wadancan mutane shi ya sa malam ya fita. Kuma na fada a rubuta ko an yarda ko ba a yarda ba Rabi’u Musa Kwankwaso ya ba wa APC gudummawa kaso casa’in da tara cikin dari , kuri’ar da Rabi’u Musa Kwankwaso ya ba wa APC ta ba wa Buhari ya zama shugaban kasa a yanzu da kuri’ar da Rabi’u Kwankwaso ya ba wa APC ta kafa mulki a Kano ko ka ki ko ka so in za a ba da minister a Kano in dai jam’iyya ce da take da adalci a nemi shawarar Kwankwaso. Mutanen nan mu muka san su mu muka zauna da su. Ni Yakubu Yarima na taba bin Buhari kwana talatin da wani abu cur ban dawo gidana ba kuma Malam Ibrahim Sheakarau ne ya tura mu duk shari’ar da ake yi da mu aka yi. Haka duk shari’ar da aka yi malam Ibrahim Shekarau ya dauki nauyinta kuma kowa yasan shari’a da kashe kudi ba kuma da kasa ake yi ba kuma malam shekarau ba gona ce da shi ba da yake noma kudi to me yasa ba a yi maganar wadannan kudin ba. Muma muna nan lokaci zai yi za mu fada sai maganar miliyan ishirin da biyar ta siyasa. Yanzu Buhari yana son ya fada mana Amaechi kudin da ya kashe wa APC a gonar lemo ta garinsu ya samu ko a gonar kwakwa ko Tinubu ko Atiku da ma kudin da ragowar gwamnonin suka kashe ya zama shugaban kasa duk a aljihunsu ne Buhari na neman ya raina mana hankali ya ce a a katin da aka dinga aikawa dari, dari biyu, shi ya sa ya ci zaben? Ai yanzu ga wani zaben nan ya zo za mu gani a ci zaben mu gani. Kuma Alhamdulillahi duk abin a suke yi a idon jami’an tsaron suke yi. Kuma munan nan muna hada data da jiragen saman da aka saya da sauransu duk muna kallo.

Don haka mu kashe wannan maganar don Allah su Injiniya Rabi’u Kwankwaso jam’iyyar APC ta bata musu ta mayar da su saniyar ware da ma abin da muka fada musu Kenan suka ce a’a to yanzu sun je sun gani da ma sun ce Jiki magayi saboda haka muna maraba da shi ya zo mu hada karfi da karfe Kano ko ba ka so dole ka bar wa mutum biyu in dai a batun siyasa ne ko dai gidan Malam Shekarau ko gidan Kwankwaso Allah ne y aba su in dai siyasa z aka yi.Kuma mu zuba ido mu gani in dai wadannan mutanen suka hada kansu ma ga me APC din za ta samu a Kano. Ba na ji Gwamnan yana wani surunbahani ba wai zai samo musu kuri’a miliyan biyar ba ko kaso daya cikin biyar muna nan da ku ba zai iya samu ba domin Rabi’u Musa Kwankwaso ba ya tare da shi sannan Dr Malam Ibrahim Shekarau ba ya tare da shi su ne masu siyasa su ne masu jama’a su ne masu jihar Kano su suke taimakon al’umma su suke gina al’umma su suka yi wa al’umma aiki.

 

To ya ka ke gani wajen tsayar da ’yan takara a jam’iyyar ba ka ganin za a sami matsala?

Ai mu damukwaradiyya za a yi ba wata rigima. Fatanmu dai Allah ya hada mana kawunan wadannan mutanen guda biyu Malam Ibrahim Shekarau da Injiniya Dr Rabi’u Musa Kwankwaso Allah ya hada mana kawunansu kawai. Ba ku ga tunda ku ka shigo masu jajayen huluna sun mamaye ko’ina ba? Da mutanen Rabi’u Musa Kwankwaso da su muka je EFCC da su muka je kotu tare da su aka buga mana tiya gas tare aka doke mu tare aka hantare mu tunda muka dawo kullum kungiyoyi ne na kwankwasiyya suke zuwa suna yi mana jaje da fatan alheri. Mu ba mu da wata rigima fatanmu dai su hada kan kawai. Da mun hadu ina tabbatar muku da wannan gwamnatin ta likimoniya tuni za su kai kasa za ka daina jin duriyarsu hatta gwamnatin tarayyar z aka daina jin su. ‘Yan takarar gwamna kuma za a yi damokuradiyya. Ai tuni su ‘yan Kwankwasiyya sun dau layi tunda ya ce Malam Sagir Takai Nakiya ce mai kyau da zaki amma sai aka dora ta a kan juji ka ga Kenan akwai wani mutum kenan a PDP da tuni ‘yan kwankwasiyya sun yarda da shi sun yi amanna da shi sun yarda da ingancinsa. Don haka muna maraba da Maigirma Rabi’u Kwankwaso a PDP.

 

An ce ai Malam Sagir Takai ba ya Gidan Sardauna.

To yanzu na ji a bakinku kuma ni ne kat tun shekara takwas da aka yi a gwamnati shekara shida na yi ina mataimakin maigirma sardauna a harkar siyasa. Da ya zama minister da yake sardauna har yanzu in ne dai ko mataimaki ba a nada min ba. Duk abin da ya shafi siyasar Sardauna ko a Kano ko a Najeriya na san kome zahiri da badini. Ba wai irin dan kidanki na jiyo ba ne ba ya taba zama harkar siyasa ba na nan in kuwa ka ga ya zauna ba na nan to ya yarda da uzirna. Don haka malam Sagir Takai yana tare da malam Shekarau yana biyayya da Malam Shekarau dan gidan Malam Shekarau ne. Malam shekarau tunda Malam Sagir ke fitowa Malam Shekarau shi yake nunawa sai a wannan lokacin shi ma don ‘ya’yan Malam Shekarau sun yi yawa har da ma wadanda ba mu yi tafiyar ANPP da su ba saboda mutum ne shi mai mutunci mai yakana mai adalci mai sanin ya kamata sai ya tara duk ‘yayansa ya ce to yanzu kun yi yawa a da ba ku da yawa da zan iya nuna mutum daya don haka kowa ya je ya yi tallan kansa kowa ya je tashi ta fisshe shi duk wanda aka fitar shi zai mara masa baya. Kuma amma sai ka tambayi al’ummar jihar Kano ka ga wa ya fi dacewa ya zama gwamnan Kano.

 

Ba ka ganin gurfanar da Shekarau a gaban kotu zai dakushe farin jininsa?

Ai ba wanda ake zuwa kotu da magoya baya kamar Malam Sheakarau . A tarihin Najeriya babu dan takarar da ake yi wa haka. Ai an kakkama mutane wasu sun yi gwamna wasu sun yi ministoci wa ye mutane suka taru akan shari’arsa miliyoyi don kawai su yi solidaritie dominsa. Randa muka shiga kotu lauyoyi sun fi dari biyu kowa ya zo da tima-timan littattafai don malam Shekarau. Akwai barista Faruk Iya rabon da ya shiga kayan lauyoyi ya fi shekara ishirin amma ranar da suit ya shiga kotu.

 

An ce da a ka yi maganar beli mutane sun yi ta kawowa. Shin gaskiya ne?

Malam Ibrahim Shekarau ake fada maka sardauna ne fa! Ai a gabana akwai mutumin da ya zo daga singa ya zo da kudi naira miliyan ashirin da biyar a motarsa ya sa a kira ni ya ce Yarima ga kudin nan. Kuma wallahi bai shiga gwamnatinmu ba kuma wallahi a gwamnatinmu ba a taba ba shi kwangila ba kuma wallahi babu wani abu da ya taba tahowa daga malam shekarau ya same shi kai taye ba amma ya ce a lokacin malam shekarau ya fara kasuwanci kuma har kasuwancin ya habaka a lokacin saboda kudi na zagaya wa an zo an yi ciniki arziki na zagayawa. Amma da na fadawa sardauna ya kira shi ya yi godiya sannan ya ce ba zai karba ba don bai ci kudin ba. To me ne na mamaki don an kawo satifiket din gidaje, mutanen Kano sun fito da kudi mutane sun fito suna ta dafifi ai malam ya taimaki al’umma, mutane na tare da Malam.

 


Advertisement
Click to comment

labarai