Connect with us

LABARAI

A Na Zargin Wata Mata Da Kashe Kishiyarta A Kano

Published

on


Wata matar aure a Karamar Hukumar Nasarawa da ke jihar Kano an zarge ta da kashe kishiyarta mai suna Mariya a unguwar Hotoro da ke Kano. An ce wannan lamari ya samo asali ne daga rashin fahimmatar juna a tsakanin ita wannan mata da kuma Marigayiya Mariya wacce a ka zargi abokinyar zamanta da yin taron dangi ita da ’ya’yanta wajen rufar wa marigayiyar wadda har sai da rai ya yi halinsa.

Haka kuma an rawaito mahaifin marigayiyar na bayyana wannan abu da abin damuwa da takaici da kuma mamaki na yadda wannan abu ya faru na rasa diyarsa, wacce a ke zargin kishiyarta da ’ya’yanta da yin taron dangi na duka da ya yi sanadin rasuwar marigayiya Mariya a unguwar Hotoro  da ke Kano, inda kuma ya nemi hukumomi da su tabbatar da yi mu su adalci a kan wannan lamari mai tada hankali.

Haka kuma bayanai sun tabbatar da cewa, yanzu haka matar da ta jagoranci wannan aika-aika da danyen aiki na hannun hukumomi, domin cigaba da bincike kan wannan lamari na zargin kishiya da kashe kishiyarta. Sai dai kuma wakilinmu ya yi kokarin jin ta baki kakakin rundunar ’yan sanda na jihar Kano, SP Magaji Musa Majia, kan halin da a ke ciki, amma abin ya ci tura.

Haka kuma a wani labarin mai kama da wannan an zargi motoci musamman masu dakon Pure Water da yin zirga-zirga ba tare da motocinsu na da birki ba wanda hakan ya na kawo hadari da ya ke sanadiyyar karairaya mutane a hanyoyi wanda ko a wannan lokaci sai da motar dakon Pure Water ta karya wani mai tallen kayan mota a mahadar titina da ke Gidan Buhari a Titin Zoo Road da ke Kano.

 


Advertisement
Click to comment

labarai