Connect with us

LABARAI

2019: An Kama Bakin-Haure Sama Da 300 –Farfesa Yakubu

Published

on


Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta bayyana cewa, jami’an kula da shige-da-fice sun damke bakin-haushe ’yan wata kasa sama da 300 da a ka kama sun a kokarin yin rajistar damar kada kuri’a a Najeriya.

Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, ne ya bayyana haka a wani taron wayar da kai da wasu kungiyoyi su ka shirya ga masu ruwa da tsakin zabe ranar Alhamis a babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja.

Kungiyar Kula da Batutuwan Zabe ta TMG, sai kuma DFID da B2P ne su ka shirya taron, inda Yakubu ya ce ya zuwa yanzu jam’iyyu 138 ne su ka nemi a yi musu rajista a matsayin jam’iyyun siyasa.

Baya ga wannan kuma ya bayyana cewa, sama da jam’iyyun siyasa 100 ne a ke sa ran za su fito takarar mukamai daban-daban a zaben 2019.

“Ya zuwa ranar 24 Ga Mayu an samu karin yi wa mutane miliyan tara rajista a kasar nan. Wannan ya karo adadin wadanda ke da rajista a Najeriya sun kai kimanin milyan 80 kenan.

“INEC ta na hada kai da karfi da jami’an tsaro domin dakilewa da bincike da damke masu sayen kuri’u da kudin a lokacin da a ke zabe,” in ji Yakubu.

A karshe ya ce, INEC ba ta da karfin ikon da za ta hana kowace kungiya fitowa ta yi rajistar zama jam’iyya matukar dai ta cika sharuddan da doka ta gindaya na yin rajistar jam’iyya.

Idan ba a manta ba, a farkon wannan shekara INEC ta tabbatar da cewa yawan jam’iyyun siyasa ba zai kawo wa hukumar wani cikas yayin gudanar da zaben 2019 ba.

A wata sabuwa kuma, hukumar zaben ta yi kakkausan gargadin cewa za ta yi amfani da jami’an tsaro domin ta cafke kuma ta ma ka duk wanda ta kama ya na sayen kuri’u a zaben gwamnan jihar Osun da za a gudanar nan gaba.

Kwamishinan INEC na Jihar Osun, Olusegun Agbaje, ne ya bayyana haka a cikin wannan makon a lokacin da ya ke taron ganawa da shugabannin jm’iyyun siyasa dangane da shirye-shiryen zaben gwamnan jihar Osun da za a yi a ranar 22 Ga Satumba, 2018.

Agbaje ya ce INEC ta shirye tsaf domin ta gudanar da sahihi kuma ingantaccen zabe, wanda zai karbu hannu biyu daga kowane bangare. Ya cigaba da cewa za a yi amfani da na’urar nan ’yar-kure domin tantance masu kada kuri’a, wato Card Reader.

Ya ce rashin nuna da’a da dattakon da ’yan siyasa ko jam’iyyun siyasa ba su yi wa dimukradiyya, abu ne mai matukar illa ga tsarin zabe. Don haka sai ya yi kira da jam’iyyu su rika nuna kawaici da dattako domin cigaban tsarin dimukradiyya.

Ya ce abin damuwa ne ganin yadda wasu ’yan siyasa ba su da wani jarin kara wa dimukradiyya nagarta, sai ma kokarin kawai su sai sun ci zabe ko da tsiya. Agbaje ya ce haifar da tashin hankali da dabanci a lokacin zabe abubuwa ne masu lalata nagartar tsarin dimukradiyya.

Ya ce da masu satar akwati da masu sayen kuri’u su ma wani bangare ne da ke illata tsarin zabe.

Daga nan sai ya ce duk wanda ya sake a ka kama shi ya na sayen kuri’un jama’a, to ya kuka da kansa. Ya ce jami’an tsaro za su damke shi kuma a maka shi kotu domin ya zama darasi ga wasu.


Advertisement
Click to comment

labarai