Connect with us

LABARAI

Siyasar Kumbotso Tsakanin Matasa Da Masu Ganin In Ba Su Ba Sai Dai Ta Watse

Published

on


Dimokaradiyyar Nijeriya kullum kara mallakar hankalin kanta take, musamman idan aka yi la’akari da yadda jama’a ke kara samun wayewa ta fuskar lalubo wanda suka hakikance da cewa zai kula da harkokin ci gaban rayuwarsu. Hakan ta sa yanzu jama’a suka sanya tabaron hangennesa domin zakulo mutanen da suke ganin idan an zabesu kwalliya na iya biyan kudin Sabulu.

Lamarin wakaci wa tashi wajen dafe madafun iko yafi yawaita a wakilcin Kananan Hukumomi, walau a matakin Jiha ko tarayya, domin nan ne idan an zabi wakili da zarar an rantsar dashi sai ya sake wurin fira da abokai, ya yiwa wadanda suka zabeshi dimbar karan mahaukaciya. Saboda haka jama’a ganin demakaradiyyar Nijeriya ta fara Balaga ya sa ya yanzu sai sun baje halayyar mai bukatar sahallewar al’umma a kowane mataki kafin amincewa da ba shi irin wannan dama.

Karamar Hukumar Kumbotso Karamar Hukuma ce da ke cikin kananan Hukumomin kwaryar birnin Kano takwas da ake kallo a matsayin madubin siyasar Kano, amma abin takaici wakilan da ake zaba sun mayar da al’ummar Karamar Hukumar wasu gidadawa, wadanda sai zabe yazo ake waiwayarsu. Ganin yanzu an fara kada kugen siyasar shekara ta 2019 masu zawarcin keujeru iri daban-daban sun fara bayyana maitarsu a fili, hakan ya sa jama’a yin duban tsanaki kafin bai wa kowane dan takara fuska.

Ganin Mai girma  shugaban kasa ya amince da gyaran dokar shekarun tsayawa takara a Nijieriya, Yanzu al’ummar karamar Hukumar Kumbotso sun shata layin cewar shekara ta 2019 ta matasa ce. Wannan ta sa

Kungiyoyi da dandazon al’umma suka ce ba wanda za su amince da wakiltar su a majalisar dokoki ta Jihar Kano sai Matashi Alhaji Abubakar Salisu Kadawa, gogaggen dan Kishin kasa, mai kaunar ci gaban matasa, wanda ya yi suna wajen tallafawa marasa galihu musamman marayu da masu bukata ta musamman.

Wannan Matashi kamar yadda aka tabbatar sai da aka kai ruwa rana kafin ya amince da bukatar al’ummar Kumbotso na fitowa takarar kujerar Majalisar dokokin Jihar Kano mai wakiltar karamar hukumar Kumbotso, an ji yadda sai ta kai ga matasa sun gama shirin gurfanar da shi gaban kuliya matukar ya ki amsa wannan kira.

Wani abin mamaki ga wannan bawan Allah shi ne yadda  bai taba rike wani mukami a siyansce ba, amma alhairansa sun mamaye karamar hukumar Kumkotso da kewaye, duk wanda ya kwana kuma ya tsahi a karamar Hukumara Kumbotso ya ga irin gudunmawar da Alhaji Abubakar Salisu Kadawa ya bayar musamman a lokacin azumin watan Ramadan da ya gabata, haka kuma ga wani tsari da ba’a taba ganin wani dan siyasa a karamar Hukumar  Kumbotso ya taba gwada haka ba, inda ya yi ruwan kayan abincin sallah ga al’umma, sannan kuma anga irin gudunmawar kayan sallah da ya rabawa marayu a karamar Hukumar  Kumbotso domin rage masu radadin maraicin da suka gamu dashi.

Yanzu haka Labari ya fantsama cikin karamar Hukumar Kumbotso cewa wannan bawan Allah ya gama shirin raba offer ga matasan karamar hukumar Kumbotso, wannan ta sa matashin dan siyasar ya gabatar da wani tsari na ziyartar matasa a wuraren sana’arsu domin taya su murnar kammala azumin watan Ramadan. Wannna ziyara ta farantawa matasa rai

domin akwai masu cewa su rabonsu da wani wanda suka zaba ya tuna da ziyartar su har sun manta, amma yanzu sai ga wannan bawan Allah ya yi

tattaki kafa da kafa har wuraren sana’ar mu ya taya mu murna. Saboda haka suka  ce tsakaninsu da Abubakar Salisu Kadawa mutu ka raba.

Wasu masu hangen nesa cikin dattawan karamar hukumar Kumbotso sun bayyana cewa sun jima basu ga matashi mai ladabi tare da girmama na gaba kamar Abubakar Kadawa ba, domin ya bambanta da sauran wadanda idan ka gansu a kafar gidanka sai lokacin da bukatar ka ta taso, idan bukatarsu ta biya shi kenan sai ayi dibar karan mahaukaciya da kowa, a koma otal da gidajen shakatawa nan ne wurin haduwarsu.

Babban abinda ake jira yanzu shi ne yadda matasan zasu kara himmatuwa wajen tabbatar da ganin ana damawa da su a harkokin wakilcin jama’a, tare da janyo kowa da kowa ba tare da banbancin akida, yare ko inda ka fiato ba.

 


Advertisement
Click to comment

labarai