Connect with us

LABARAI

Rikicin ANMFO: Rarara Bai Ci Ko Kwabo Ba  –Murtala Mamsar

Published

on


An bayyana cewa fitaccen mawakin Siyasar nan a Nijeriya kuma Shugaban Amintattu a Kungiyar Mawakan Arewa na Jam’iyyar APC, [ANNMFO], Alhaji Dauda Kahuta Rarara bai ci ko kwabon kungiyar ba, kamar yadda wadansu mawakan suke yayatawa a kafofin watsa labarai.

Wannan bayanin na kunshe ne a jawabin da mataimakin shugaban na kasa, Alhaji Murtala Mamsar Jos ya sanar a wani taron ‘yan Jarida da ya kira a Jos fadar gwamnatin jihar Filato, ran Labaran da ta gabata.

Ya ce sanya mutane masu mutunci kamar irinsu Gwamnan jihar Zamfara, Alhaji AbdulAzeeze Yari a cikin maganar ba daidai ba ne, kuma ma maganar ba haka take ba, domin Dauda masoyi ne ga dukkan mawakan ANMFO.

Ya ce bisa daukakar da Allah ya yi masa a sanadiyar nasarar da ya samu na hada kan ‘ya’yan kungiyar ya sa suka zama tsintsiya madauriki daya na haifar da akhairai ainun wa ‘ya’yan kungiyar a yanzu, domin ya baiwa shugabannin kungiyar dammar saduwa da Gwamnoni Arewacin kasar nan kai tsaye domin su gabatar masu da koke-kokensu.

Ya ci gaba da bayyana cewa daga cikin wadanda suka riga suka sadu da su, sun hada da Gwamnonin jihohin Kaduna, Katsina da Zamfara, inda suka amince za su taimaka wa kungiyar.

Murtala Mamsar ya ci gaba da bayyana cewa, amma abin mamaki ba a kai ko’ina ba sai ga shi ana ta yayatawa cewa wai Shugaban Amintattun ya karbi kudi a hannun Gwamnan jihar Zamfara, AbdulAzeez Yari, ana ta zagi ana cin mutunci, har ma wadansu na cewa wai Naira miliyan 60, wadansu na cewa Naira miliyan 100, wadansu ma na cewa Naira miliyan 180.

Ya kara da cewa mutane irinsu Abubakar Sani da Haruna Aliyu Ningi da a can ba ‘ya’yan wungiyar ba ne, sun shigo ne kawai da burin wargaza kungiyar, wanda ya ce ba za su yi nasara ba idan Allah ya so.

Daga nan sai ya bayyana cewa Alhaji Rarara ba zai ta ba yarda da duk abin da zai taba mutuncin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ba.

Daga nan ya jawo hankalin ‘ya’yan kungiyar masoya Muhammadu Buhari da su yi watsi da irin labaran da suke sauraro a gidajen wasa labarai da wadanda suke karantawa a jaridu na cewa shugaban amintattu na kungiyar ya yi awon gaba da wadansu kudade na ‘yan’yan kungiyar.

Murtala Mamsar ya kuma fayyace cewa Dauda Rarara ba zai ce uffan ba, sai idan mutumin da yake da shaidar

ya ci kudin kungiyar, to ya zo ya tinkare shi da shaidar ya ci kudi sannan zai ce wani abu.


Advertisement
Click to comment

labarai