Connect with us

LABARAI

NIS Ta Gargadi Mutanen Ketare Kan Shiga Harkar Zaben Nijeriya

Published

on


Shugaban Hukumar shige da fice ta kasa, Muhammad Babandede MFR, ya tsinkayi sanarwar da ke yawo a wasu kafafen yada labarai masu zargin cewa, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC, na duba yiwuwar yi wa wasu mutanan wajen kasar nan rajistan yin zabe kafin nan da babban zaben 2019.

Cikin wata sanarwa da ta fito daga kakakin hukumar ta shige da fice, DCI Sunday James, ya bayyana cewa, “Yana da matukar mahimmanci a bayyana cewa, daga cikin aikin hukumar shi ne lura da bakin hauren da ke cikin kasar nan, hukumar ta shigi da fici tana bayar da tabbacin cewa, babu wani bakon hauren da aka yi wa rajistar zabe a kasar nan.

Hukumar ta shige da ficen ta kara da bayyana cewa, “Baya ga jami’anmu da muka tura su kula da yadda lamurran siyasar namu ke tafiya, domin tabbatar da cewa, ba wani wand aba dan kasan nan ba da ya tsalma mana baki kan harkokin siyasarmu, hakanan, al’adar hukumar ce ta shigi da fici, su rika ayyukan wayar da kan al’umma domin hana wadand aba ‘yan kasannan ba shiga dukkanin harkokin mu makamantan hakan.” Yana kuma da mahimmanci a lura da cewa, hukumar ta shigi da fici, tana da alakar aiki mai kyau a tsakaninta da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, tana kuma da bayanan duk abin da ke gudana domin tabbatar da cewa mutane musamman ma wadand aba ‘yan kasannan ba, ba a bas u damar kaiwa ga duk wani bayanin da mu ya shafa ba kai tsaye.

Don haka yana da mahimmanci a san cewa, ‘yan Nijeriya nagari da ke aiki a hukumar ta shige da fice, suna aiki tukuru na ganin ba wani wanda ba dan Nijeriya ba da ya tsalma bakinsa musamman ma na babban al’amari da ya shafi hukumar ta zabe, duk kuma wani wanda ke da wata kwakkwaran shaidar da ke iya tabbatar da cewa akwai wani wanda ba dan Nijeriya ba da ke shiga harkokin zabenmu, da ya hanzarta sanar da hukumar domin hanzarta daukan matakin da ya dace.

 


Advertisement
Click to comment

labarai