Connect with us

LABARAI

Minista Ya Kaddamar Da Sabon Shirin Kiwon Lafiya Na Gwamantin Ganduje

Published

on


Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya jagoranci bikin kaddamar da wasu shirye-shirye guda shida domin tallafawa harkokin lafiya a Jihar Kano, wanda ma’aikatar Lafiya karkashin gwamnatinsa ta bullo da su.

Gwamna Ganduje, na tare da Ministan Lafiya, Farfesa Isaac Adewale, wanda ya halarci Jihar Kano domin halartar taron NCH na shekara ta 2018.

An kaddamar da taro ranar Laraba wanda ya kunshi shirin  samar da hanyoyin kula da lafiyar al’ummar Kano, sai kuma shirin hadaka na harkar lafiya domin ma’aikatan Jihar Kano,  kaddamar da ‘yan kwamitin amintattu na  asibitin yara  na zamani, KUSH, asusun tallafawa harkar lafiya, KHETPUND, hukumar asibitoci masu zaman kansu, PHMA. Kaddamar da shirin hanyar hadaka harkar lafiya.

Akwai sama da mutun dubu biyu wanda suka yi rajista daga cikin ma’aikatan Jihar Kano  wanda iyalansu ke sa ran za su fara amfana da shirin,  wanda tuni aka cire kudaden cikin watanni biyu daga albashinsu, wanda tuni aka tura sama da cibiyoyin lafiya 230 da aka zaba.

Jihar Kano ce Jiha ta farko da ta fara aiwatar da wannan shiri a fadin kasarnan,  wanda kuma shiri ne na gwamnatin taraya da aka gabatarwa da Jihohi . Haka kuma kaddamar da hukumomin KUSH, KHETPUND, PHMA, wanda ake sa ran su fara aiki nan ba da jimawa ba.  Fara aikin wadancan manyan asibitoci biyu irin na zamani, asusun amintattun da kuma hukumar lura da asibitoci masu zaman kansu. An tabbatar dukkan wadannan tsare-tsare an shirya su ne  domin inganta harkokin lafiya a Jihar Kano, sannan kuma tsarin zai rage yawan fita kasashen waje domin neman magani.

Wadannan sabbin tsare-tsare za su daukaka darajar Jihar Kano, a kan sauran Jihohin kasarnan ta fuskar harkokin kiwon lafiya, Sauran ayyukan da aka kaddamar a wannan rana sun hada da  shirin hadin guiwa tsakanin gwamnatin Kano da USAID, wanda zai lura da matsalar tarin fuka a fadin Jihar Kano, wanda ake zaton akwai shi a tsakanin al’ummar garuruwa goma sha bakwai na Jihar Kano, yayin da aka tabbatar da mutane 70 sun kamu da cutar tarin na Fuka wanda tuni aka yi masu  magani kyauta. Hakazalika, shirin zai bayar da tallafin yi wa mata masu matsalar kansar nono  aiki guda dubu a Jihar Kano,  wanda za a gudanar a sibitin Muhammadu Buhari da ke Giginyu.

Babban bako a wurin taron, Ministan Kiwon Lafiya, Farfesa Isaac Adewale,  ya jinjina wa Gwamna Ganduje, bisa kokarinsa musamman a harkokin da suka shafi lafiya, Farfesa Adewale, ya ci gaba da cewa, Gwamna Ganduje, ne zakaran gwaji a tsakanin takwarorinsa, musamman wajen sauraron al’ummarsa, musamman yadda ya dauki kalubalen ‘yan adawa a matsayin ma’aunin ci gaban ayyukansa na alhairi, Farfesa Adewale, ya ce, “lokacin da wasu gwamnonin ke rokon ma’aikatar lafiya ta tarayya ta  kawo masu dauki, Jihar Kano karkashin Gwamna Ganduje a kodayaushe  na kiran mu domin zuwa mu ga ayyukan da ya samar a fannin lafiya wanda na gane wa idona”, in ji shi.

Taron wanda ya samu halartar Mai Martaba Sarkin Kano,  Malam Muhammadu Sanusi II, da ‘yan majalisar Sarkin, Sakataren hukumar inshora ta kasa, abokan hadin guiwa, jami’an gwamnatin Jiha da na tarayya da sauran manyan baki ne suka  halarci muhimmin taron.


Advertisement
Click to comment

labarai