Connect with us

LABARAI

Addu’a Ce Ta Saukaka Musifun Da Suka Auku A Bauchi –Shugaban Buhari

Published

on


A jiya Alhamis Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi tattaki zuwa jihar Bauchi domin jajanta wa illahirin jama’an jihar dangane da musifar Guguwa da kuma wata mummunar Gobara da ta kone babbar kasuwar Azare gabaki daya.

Bayan saukarsa daga jirgin sama a filin sauka da tashin jirage na Sa Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi, shugaban kasan ya fara nausawa zuwa babbar kasuwar Azare da ke karamar hukumar Katagum ta Jihar Bauchi domin gane wa idonsa irin barnar da Gobarar ta yi a ranar Lahadin da ta gabata.

 

Bayan dawowarsa, ya yi bayani a fadar gwamnatin jihar Bauchi, inda ya bayyana cewar, ya zo jihar ne domin jajantawa da kuma nuna damuwarsa kan yadda wannan lamarin ya wakana.

Buhari, ya bayyana cewar addu’a ce kadai take kawo saukin irin wannan ibtila’in, don haka ne ya nemi jama’a su ci gaba da kara rungumar addu’a.

Muhammadu Buhari ya ce; “Dalilin da ya kawo ni jihar Bauchi a yau shi ne domin na jajanta dangane da ibtila’in Guguwa a cikin Bauchi da Gobara wacce ta auku a Azare. Fatanmu Allah ya kiyaye gaba.

“Wutar ta kasuwa da aka yi na je da kaina na ga wurin ana iya cewa kasuwar ta kone kurmus da kuma dukkanin abun da ke cikinta. Allah ya maida abun da ya fi haka, kuma Allah ya bamu damina mai albarka,” In ji Buhari.

Shugaban ya kara da cewa; “Sai a yi hakuri wadannan abubuwan sun fi karfin mutum, sai dai addu’a, addu’o’in da ake yi su ne ke taimakawa abubuwa su zo da sauki. Watakila da ba a yin addu’ar musifar da ta fi haka, Allah ya kara karbar addu’armu, Allah ya bada hakuri,” Kamar yadda ya shaida.

Shugaba Buhari, ya kuma bukaci, Sarkin Bauchi, Gwamnan Bauchi da sauran wadada suke wajen da su isar da sakon jajensa ga jama’an jihar ta Bauchi dangane da wannan lamarin, ya kuma nuna gayar damuwarsa kan yadda ya gane wa idonsa yadda barnar ta yi, “Sannan, a ida jajena ga sauran al’umman da abun ya shafa; Allah kuma ya kiyaye na gaba”.

Tun da fari, gwamnan jihar Bauchi Muhammad Abdullahi Abubakar wanda shi ne ya tarbo shugaban kasan, ya fara ne da bayyana irin yadda ibtila’in ta auku wa jama’an jihar ta Bauchi.

“Muna gode wa Allah da ya ba mu ikon amsar bakwancin shugaban kasa a yau. Hakika, tun kafin shugaban kasa ya zo mun yi magana da shi ta waya, inda ya nemi a jajanta masa ga dukkanin illahirin jama’an Bauchi da wadannan ibtila’in biyun ta shafa. Nan take kuma na isar da sakon da shugaban kasa ya bani,” In ji Gwamnan.

Ya ci gaba da bayyana yadda shugaban kasar ya damu gaya kan lamarin; “bayan haka, mai girma shugaban kasa ya kuma kira waya da kansa inda ya yi wa Saraukunan da abun ya shafa jaje. Bayan haka ma, yau gashi ya taso takanas ta kano ya zo jihar Bauchi domin ya jajanta. Wannan ya nuna mana yadda soyayyar da ke tsakanin shugaban kasar Nijeriya da al’umman jihar Bauchi gabaki daya,” In ji Gwamnan.

Gwamnan Bauchi, ya yi godiya a bisa karamcin da shugaban kasan ya yi wa jama’ar jihar domin zuwa ya gani da idonsa kan musifu guda biyu da suka auku a jihar ta Bauchi.

Da yake maraba da shugaba Buharin, Sarkin Bauchi Alhaji Rilwanu Sulaiman Adamu ya nuna godiyarsa kan yadda shugaban ya damu gaya kan lamarin da ya auku a jihar.

Sarkin ya yi bitar irin ibtila’in da ya auku a jihar, inda ya bayyana cewa al’umman jiharsa sun samu jarabawa ta aukuwar bala’ai har guda biyu, inda ya bayyana cewar Guguwa ta yi barna sosai wa jama’an jihar Bauchi a ranar Asabar wanda hakan ya janyo asaran rayukan jama’a da kuma muhimman kayayyaki da dukiyoyin miliyoyin naira, muhallai da sauransu, lamarin da ya shafi dubban gidaje da dubban jama’an jihar.

Ya kuma bayyana cewar a ranar Lahadi kuma aka sake samun wata mummunar Gobara a babban kasuwar Azare, inda ya bayyana cewar wannan kasuwar babbar kasuwa ce a cikin kasuwannin da suke kasar nan, ya bayyana cewar wannan kasuwar an samu asarar miliyoyin naira a sakamakon Gobarar.

Daga bisani Sarkin ya mika godiyar jama’an jiharsa kan ziyarar da shugaban kasar ya kawo wa jama’an jihar.

LEADERSHIP A Yau Juma’a ta nakalto cewar a ranar Asabar da ta gabata ne jama’ar Jihar Bauchi suka gamu da wani irin ruwan sama mai karfin gaske hade da iska mai tsanani, lamarin da ya janyo ruguza dubban gidajen jama’an jihar. Guguwar wacce aka kiyasce cewar ta shafi kashi biyu na cikin ukun gidajen da suke Jihar Bauchi ta ratsa kowace unguwa a cikin jihar.

Guguwar ta haddasa asarar miliyoyin naira, shaguna, gidaje, massalatai, coci-coci, ma’aikatu, muhallan gwamnati da sauran muhimman wurare, baya ga haka, uwa uba ma Guguwar ta ci rayukan jama’an jihar da dama domin gine-gine sun fado kan wasu da dama a unguwanni daban-daban. Kawo yanzu babu wata hukumar da ta shaida yawan mutanen da suka rasa rayukansu a kan wannan ibtila’in Guguwar a cikin Bauchi, sai dai wasu rahotonni sun bayyana cewar an samu mutuwar mutane 40, wasu rahotonnin ma suka ce adadin ya fi haka.

Wakilinmu ya shaida cewar, ita dai wannan Guguwar ba a taba samun irinta a Jihar Bauchi ba saboda muninta, amma kuma bincikenmu ya gano cewar a ‘yan watannin baya samu ire-iren Guguwar kamar a kauyen Duguri inda Guguwar ta lalata gidaje sama da 200, da kuma asarar rayuka, da dukiyoyin jama’a.

Haka kuma a wasu kauyeka da dama su ma an samu irin wannan Guguwar a Jihar Bauchi.

Dangane da musifar Gobara a garin Azare da ke karamar hukumar Katagum kuwa, Gobarar ta cinye dukkanin shagunan da suke cikin babbar kasuwar inda kuma ta lakume miliyoyin naira da kayyakin ‘yan kasuwa.

Bincikenmu ya gano cewar wannan dai shi ne karo na uku da ake samun irin wannan ibtila’in Gobara a wannan kasuwar ta Azare, sai dai wannan Gobarar ita ce mafi muni ga jama’ar garin.

A karshe dai wakilinmu na Bauchi, ya shaida cewar Shugaban Kasa Buhari na kammala ziyarar jajen ya juya domin zuwa komawa babban birnin tarayya Abuja.


Advertisement
Click to comment

labarai