Connect with us

LABARAI

Kusan Jinsin Jininku Kafin Yin Aure –Sarkin Gwandu

Published

on


Sarkin Gwandu, Alhaji Muhammadu Iliyasu Bashar kuma shugaban majalisar sarakunan jihar kebbi ya kira ga ma’aurata da susan nau’in jininsu kafin yin aure a tsakanin junna.
Sarkin ya kiran ne yayin da yake karbar tawagar mambobin kungiyar sikila a jihar ta Kebbi da a ke kira a turance “kebbi State Sickle Cell Association (KESCA)”,a fadarsa ta Abdullahi fodiyo falas da ke a Birnin-kebbi a jiya .
Yayin da shugabar kungiyar ta jihar Hajiya Hadiza Yahaya Shantali ta jagoranta zuwa fadar maimartaba sarkin Gwandun domin Kai masa ziyarar bangarma da kuma neman goyun bayansa ga yekuwar da kuma wayar da kan da kungiyar keyi na ganin cewa ta rage cutar nan ta ciwon sikila a cikin jama’ar jihar ta kebbi.
Sarkin na Gwandu ya ci gaba da cewa akwai bukaci iyaye su tabbatar da cewa kafin su bada ‘ya’yansu ga aure, sun yi awon jini domin Susan nau’in jinin da kuma lafiya kansu kafin gudanar da aure ga ‘ya’ya nasu domin a samu saukin magance matsalar cutar sikila a cikin jama’a da kuma ‘ya’yasu da a ke kira “sickle cell “a turance .
Bugu da kari sarkin yace “ Idon muna da karfin iko , da duk sarakunan mu za suyi umurni don gwajin jini ga dukkan ma’aurata kafin gudanar da aure a tsakaninsu domin su san irin kwayar halittar su don kwace wa zama marasa lafiya daga cutar sikila da sauran cututtuka kamar cutar HIB “.
Kazalika sarkin na Gwandu, ya ya bawa kokarin da kungiyar keyi yekuwa da kuma wayar da kan jama’a game da cutar sikila da kuma yadda za a gudanar da gwajin jini ,ya kuma ya yi kira ga a sanya wannan a cikin doka ta zama wajibi ga ma’aure sai su san jinsin jininsu kafin yin aure.
Da take gabatar da jawabin ta tun farko, Shugabar kungiyar Hajiya Hadiza Yahaya Shantali ta bayyanaw wa Sarkin na Gwandu cewa “ a matsayin yau ranar bukin masu dauke da cutar sikila ta duniya da ake kira “Sickle cell “ na Shekare ta 2018, kungiyar Sickle cell ta jihar kebbi da kuma wasu ƙungiyoyi masu zaman kansu a jihar sun shirya tafiyar kasa na sikila tare da gabatar da takardun kasida a kan bukatar su ba da kulawa na musamman ga mutanen da ke rayuwa tare da ciwon sikila da kuma kaddamar littafi kan ayyukan kungiyar “kebbi State Sickle cell Association “(KESCA) a Kebbi, da kuma ziyara ga sarkin Gwandu da fadar gwamnatin jihar kebbi domin bayyana musu muhimmancin wannan rana bukin Sickle cell ta duniya ta shekara ta 2018 a jihar kebbi da sauran jahohin duniya baki daya ke gudanar wa ayau.
Bugu da kari Hajiya Hadiza Shantali ta kara bayanin cewa “an kafa kungiyar ne a shekara ta 2003 kuma an yi
mata rajista ga Hukumar kula da rajistar kungiyoyi da kuma kamfunnan Kasuwanci ta kasa watau “Corporate Affairs Commission” don tallafa wa mutanen da ke fama da ciwon sikila kuma don wayar da Kai da kuma samar da gwajin jinsin jini ga ma’aurata da kuma basu shawarwari ta yadda zasu zauna lafiya batare da wata da muwaba.
Ita ma matar Gwamnan Jihar Kebbi, Dokta Zainab Atiku Bagudu a lokacin da aka gabatar jawabinta a wurin bukin kaddamar da littafin kungiyar ta sikila watau “kebbi State Sickle cell association “(KESCA)a fadar gwamnatin jihar kebbi a jiya a Birnin-kebbi a kan Sickle Cell a matsayin wani ɓangare na ayyukan da ke nuna bukin ranar Sickle Cell na Duniya, inda ta yaba wa kungiyar kan shirya wannan bukin na kaddamar da littfin ayyukan kungiyar ta sikili a jihar kebbi da kuma gangamin na wayar da kan jama’a kan matsalar nan ta sikila.
Saboda hakan matar Gwamnan ta dauki alkawarin biyan miliyan daya da dubu dari uku (1.3Miliyan ) don yiwa wata ‘yar yarinya ‘yar shekara 16 da haihuwa a duniya aiki a asibiti domain maye gurbin raguwa da yarinya tayi ga kunkurun ta kan cutar na ta sikila da ke damun ta.
Daga karshe tayi godiya ga irin kokarin da shuwagabanin kungiyar keyi na ganin cewa ta taimakawa masu matsalar cutar sikila a jihar ta kebbi.


Advertisement
Click to comment

labarai