Connect with us

LABARAI

ISIS: Nijeriya A Shirye Take Ta Dakile Duk Wata Barazana –Gwamnatin Tarayya

Published

on


Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, na ta sane da yiwuwar ‘yan kungiyar IS daga kasashen Iraki da Siriya suna shigowa kasar nan a sirrance, amma gwamnati a shirye take ta dakile duk wani barazana da shigowar tasu zai kawo.
Wannan na zuwa ne a dai dai lokacin da gwamnatin tarayyar ke bada umurmi ga hukumomin tsaro dasu tsaurara tsaro a dukka filayen jiragen sama na kasar nan su kuma kara kaimi wajen binciken ma’aikatan jiragen sama da fasinjojin dake shigowa kasar nan.
An kuma umurcesu da kara sanya ido a kan wuraren da aka hana zirga zirga a cikinsu a filayen jiragen.
Haka kuma, hukumar kula da filayen jiragen sama, FAAN, ta sanar da cewar, sakamakon labarin cewa, ‘yan ta’ada na sulalowa cikin kasar nan daga kasar Siriya ta kara tsaurara matakan tsaro a dukkan filayen jirgin saman kasar nan.
Gwamnatin tarayya ta nuna matukar damuwarta a kan rahoton dake nuna cewa, mayakan kungiyar ISIS na sulalowa cikin Nijeriya, ta kuma kara da cewa, lamarin zai zama cikin manyan abubuwan da za a tattauna a kai a taro kashi na 7 na Ministocin tsaron kasashen “Sahel-Saharan States, CEN-SAD” da zai gudana tsakanin ranar 20 ga watan Yuni zuwa ranar 22.
Babban sakatariya a ma’aikatan tsaro Misis Nuratu Batagarawa ce, ta bayyana haka a tattauna da tayi da ‘yan jarida kafin a fara taron rana Alhamis, ta ce, Nijeriya da sauran kasashen yankin Sahara na matukar famuwa da taaddancin da ake yi a iyakokin kasashen yankin.
Ta bayyana cewa, taron zai mayar da hankali ne a kan bukatar musayan bayanan sirri tsakanin kasashen domin magance aiyyukan ta’adanci tsakanin iyakokin kasashen wadanda suka hada da taadancin da rikice rikicen makiyaya da manoma da kuma yan ta’adda masu kashe mutane.
A kan sanya ido a gilayen jiragen sama kuwa, wata majiya ta shaida wa manema labarai cewa, “Wata wasika da ta fito daga ofishin sakataren gwamnatin tarayya mai lamba H.150/S.91/56, aka kuma sanya was hannu ranar 25 ga Mayu 2018, ta umurci hukumar “Nigerian Cibil Abiation Authority, NCAA da FAAN da kuma hukumar kwastam dasu tsaurara matakan tsaro a filayen jiragen sama na kasar nan gaba daya”
Mista O. M. Olaoye ya sanya hannu a wasikar a madadin sakataren gwamnatin tarayya.
Haka kuma shugaban hukumar Corporate Affairs, Henrietta Yakubu, ta bayyana was manema labarai cewar an bayar da umurnin tsaurara tsaro a filayen jirgin kasar nan ne saboda a kare aukuwar wani matsala a filayen jiragen.
Yakubu ya kara da cewa, an bayar da kulawa na musamman ne ga filayen jiragen sama na Legas da Abuja da Kano da Enugu da kuma Fatakwal saboda kasancewarsu hanyar shigowa daga kashen waje.
Ta ce, hukumar FAAN dana ABSEC suna aiki tare don tabbatar da tsaro da kuma hana shiga wuraren da aka hana shiga a filayen jiragen saman kasar nan gaba daya.
“A samar da kayan aiki na sintirin hadin gwiwa da sojoji, an kuma Samar da motoci son raka fasinjoji a lokacin da suka iso da lokacin da zasu bar filayen giragenmu.”
Yakubu ta kara da cewa, hukunar FAAN ta samar da kayan aiki na zamani domin binciken fasinjoji da kayayyakinsu kafin su shiga cikin filayen jiragen saman.
Ta ce, “ Runduna na musamman masu rusa bama bamai na nan na lura da nauran dake lura da kayayyakin jamaa, yayin da kuma hukumomin ABSEC dana NDLEA ke ci gaba da bincike a kan duk wani abin da ake zargin yana da matsala.”
Yakubu ta kuma kara da cewa, za a bi gaba da fadakarwa ga maaikata da masu amfani da fikayen giragen saman a kan hanyoyin da za su fuskanci harin taadanci musamman a wannnan lokacin da wannan barazanar ta fito.


Advertisement
Click to comment

labarai