Connect with us

LABARAI

Gwamnati Za Ta Kafa Cibiyoyin Kiwo A Jihohin Oyo, Binuwe Da Kaduna

Published

on


Gwamnatin tarayya da Jihohi, sun amince su kafa cibiyoyin kiwon shanu a Jihohi 10, Adamawa, Binuwe, Ebonyi, Edo, Kaduna, Nasarawa, Oyo, Filatau, Taraba da Zamfara, domin kawo karshen fadace-fadacen manoma da makiyaya da ke aukuwa a kasarnan.
Jihohin goma sune za a fara shirin da su.
An bayyana hakan ne a Abuja ranar Talata wajen wani taro na lalubo hanyar hana rikicin na manoma da makiyaya.
Da yake gabatar da shirin, Sakataren kwamitin na taron, Dakta Andrew Kwasari, ya ce, gwamnatin tarayya da Jihohin za su kashe Naira bilyan 70 a shekaru ukun farko na shirin.
Ya kuma ce, jimillan Naira bilyan 179 ne za a kashe cikin shekaru 10 kan aiwatar da shirin.
A watan Janairu ne mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya kafa kwamitin da zai lalubo hanyar hana rikicin na manoma da makiyayan.
A farkon watan Fabrairu ne, kwamitin ya kafa wani karamin kwamiti a karkashin Gwamnan Jihar Ebonyi, Dabid Umahi, wanda zai bayar da shawarar hanyar da za a kawo karshen rikicin.
Kwasari, ya bayyana cewa, a watan Afrilu ne kwamitin ya amince da fara aiki da wannan shawarar a wadannan Jihohin 10.
Ya ce, “an shirya samar da wasu wurare na musamman na zamani domin yin kiwon a sassa daban-daban har 94 a wadannan Jihohi 10 da za a fara da su.”
Sakataren ya ce, kamar yadda aka tsara, gwamnoni da kuma wasu al’ummu masu zaman kansu za su bayar da gudummawar filayen da za a kafa cibiyoyin kiwon.
Kwasari ya ce, za a samar da cibiyoyin ne girma-girma, akwai masu daukan shanu 30, 60, 150 da 300, a wuraren kiwon.
Sakataren ya ce, samar da hatsin da dabbobin za su ci a lokutan rani duk yana cikin tsarin da aka yi.
Ya ce, gwamnati za ta nemi ‘yan kasuwa masu zuba jari har ma da wasu kasashen da su yi binciken hanyoyin da Nijeriya za ta bunkasa kiwon shanunta da samar da nono da kuma nama cikin shekaru 10.
A yanda aka tsara shirin za a yi rajistan makiyayan ne a matsayin wasu kungiyoyin da aka amince da su domin yin kiwon.
“Kungiyoyin kuma za su ci gajiyar cibiyoyin kiwon ta hanyoyi daban-daban har ma da samar masu da basuka, hatsi da kuma rangwame kan abubuwa masu yawa.
Ya ce, “Da wannan shirin ana sa ran samun nonon shanu lita milyan 200 a shekarar farko, a shekarar shirin ta biyu kuma ana sa ran samun lita milyan 700 ne na nonon shanun a duk shekara.
Ya bayyana cewa, shirin na farko gwamnati ce za ta dauki nauyinsa, amma a kashi na uku zuwa shekara ta goma, masu zuba jari ne za su zuba Naira bilyan 100 a cikin shirin.
Ya kuma ce, za a kafa wani bankin samar da maniyyin shanun a kowace daga cikin Jihohi 10 da za a fara aiwatar da shirin a cikin su. Kamar yadda za a samar da saka maniyyin ta hanyar zamani da ababen kiwon lafiya a dukkanin cibiyoyin kiwon.


Advertisement
Click to comment

labarai